Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 409 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 43,846 tare da jikkata fiye da mutum 103,740. A ƙasar Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,480 tun watan Oktoban 2023.
Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024
0549 GMT –– Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa WAFA ya ruwaito cewa Isra'ila ta kashe mutane da dama, ciki har da yara, a harin bama-bamai da ta kai da sanyin safiya a kudancin Gaza.
Majiyoyi daga asibiti sun ce dakarun Isra'ila sun kashe mutum huɗu 'yan gida ɗaya –– wani mutum da matarsa da 'ya'yansa. 'Yarsu ta tsallake rijiya da baya amma ta samu raunuka masu muni, sakamakon luguden wutar da sojojin Isra'ila suka yi a wani tanti da 'yan gudun hijira suke samun mafaka a yankin Al Mawasi da ke yammacin Khan Younis.
Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a yankin Al Mawasi na Gazaduk da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana shi a matsayin "tudun-mun-tsira."
Mazauna yankin sun ce Isra'ila ta sha kai musu hari babu ƙaƙƙautawa.
Ƙarin labarai????
0633 GMT –– 'Wani abin fashewa' ya faɗa kudancin Jordan ba tare da jikkata kowa ba: Rundunar sojin Jordan
Rundunar sojin Jordan ta ce "wani abin fashewa" ya faɗa a yain da ke kan iyaka na lardin Aqaba da ke kudancin Isra'ila.
Wata sanarwa ta ambato majiyoyin soji suna cewa babu wanda ya jikkata sakamakon faɗuwar abin.
Ta ƙara da cewa jami'an tsaro sun isa wurin da lamarin ya faru.
Sai dai sanarwar ba ta faɗi sunan abin da ya faɗa a yankin ba, ko kuma daga inda aka harba shi. Birnin Aqaba yana daura da birnin Eilat na kudancin Isra'ila.