Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 63 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 17,000, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 46,000 sun jikkata.

KAI-TSAYE: Harin bam na Isra'ila ya kashe mutane da dama ya jikkata wasu a Birnin Gaza

1225 GMT Gaza ba za ta kai labari ba idan aka sake rasa gadon kwantar da marasa lafiya a asibiti – WHO

Tsarin lafiya na Gaza ya kusa durƙushewa kuma yankin ba zai kai labari ba idan aka sake rasa motar ɗaukar marasa lafiya ko gadon asibiti, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargaɗi.

Kakakin hukumar ta WHO Christian Lindmeier ya shaida wa taron manema labarai a Geneva cewa, "Al'amarin yana kara ta'azzara a kowace rana... fiye da zato."

"Tsarin kiwon lafiya ya durkushe. Gaza ba za ta iya yin asarar wasu cibiyoyin kiwon lafiya ba, ko wata motar daukar marasa lafiya guda daya, ko wasu asibitoci... ko ma gadon asibiti guda daya."

Lindmeier ya ce yara da mutane suna “bara kuma suna kukan neman ruwa."

"Muna kan wannan matakin, inda ba a samun kayayyakin yau da kullum da na yau da kullun," in ji shi. "A yanzu ruwan da ake samu Gaza bai wuce lita daya zuwa biyu ba a rana - wato ruwa rayuwa ne, ba kawai na sha ba. Wayewa ci gaba suna gab da wargajewa."

0702 GMT — Harin bam na Isra'ila ya kashe mutane da dama ya jikkata wasu a Birnin Gaza

Mutane da dama ne suka mutu yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani harin bam da Isra'ila ta kai a unguwar Shujaiya da ke birnin Gaza a cewar kafar yada labaran Falasdinu.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu Wafa, ya bayar da rahoton cewa, an ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a wasu yankuna da dama a Gaza.

Hukumar ta ce, Isra'ila ta fi kai hare-haren a yankunan gabashin Khan Younis da kuma gabar tekun Rafah da ke kudancin Gaza, yayin da jiragen yakin Isra'ila suka fi kai hari a tsakiyar Gaza.

A ranar 1 ga watan Disamba ne Isra'ila ta sake kai farmakin soji a Zirin Gaza bayan kawo ƙarshen tsagaita wuta na tsawon mako guda da kungiyar Hamas ta Falasdinu.

Akalla Falasdinawa 17,177 aka kashe yayin da wasu fiye da 46,000 suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da aka kai a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin ba-zata da ƙungiyar Hamas ta kai.

0400 GMT — Hukumomin Falasdinu suna aiki da Amurka kan yadda za a tafiyar da Gaza bayan yaki

Hukumomin Falasdinu suna aiki da jami'an Amurka kan yadda za a gudanar da Gaza da aka mamaye bayan yaki, kamar yadda jaridar Bloomberg News ta ambato Firaiministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh yana bayyanawa.

Abin da ake so bayan yakin shi ne kungiyar Hamas da ke rike da ikon Gaza ta zama karamar mai hada gwiwa da kungiyar Falasdinawa ta Palestinian Liberation Organization (PLO), inda za ta taimaka wurin gina sabuwar kasa mai cin gashin kanta wadda ta kunshi Gabar Yammacin Kogin Jordan, da yankin Gaza da aka mamaye da Gabashin Birnin Kudus, a cewar Shtayyeh da ke zaune a Ramallah, a hira da Bloomberg News.

"Idan (Hamas) ta shirya yin sulhu da kuma amincewa da tsarin siyasar PLO, daga nan za a samu gurbin tattaunawa. Bai kamata kawunan Falasdinawa su kasance a rabe ba," in ji Shtayyeh, inda ya kara da cewa shirin Isra'ila na murkushe Hamas gaba dayanta ba mai yiwuwa ba ne.

2315 GMT — Yunkurin ba da agajin Majalisar Dinkin Duniya ga miliyoyin mutane a Gaza na cikin garari

Jami'in kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, kokarin samar da abinci da ruwa da sauran kayayyaki ga miliyoyin mutane a Gaza ya tabarbare.

Martin Griffiths ya ce babu wani wuri a cikin yankin da ke da tsaro saboda hare-haren da sojojin Isra'ila ke kai wa ba kakkautawa a kudancin Gaza ya yi daidai da irin wanda ta kai a arewacin kasar.

Griffiths ya ce, "Abin da ke faruwa a Gaza yana tilasta wa mutanen Gaza su zabi inda za su kasance da kuma zabi kan tashin hankali - da kuma matsin lamba."

Ya ce har yanzu manyan motocin da ke dauke da kayan agaji suna shigowa Gaza ta mashigar Rafah daga Masar, amma Majalisar Dinkin Duniya da takwarorinta na kokarin gano hanyoyin da ba a binne ko lalata ba.

Griffiths ya ce MDD ta kwashe makonni tana tattaunawa don bude mashigar Karem Abu Salem daga Isra'ila domin ba da damar manyan motoci su tafi kai tsaye zuwa arewacin Gaza da kuma ta Rafah da kuma kudanci.

"Akwai wasu alamu na karfafa gwiwa a yanzu waɗanda za su iya buɗewa nan ba da jimawa ba," in ji shi.

Mazauna yankin da kungiyoyin kare fararen hula sun ceto wani yaro Bafalasdine a karkashin baraguzan gini bayan harin da Isra'ila ta kai kan wani gidan Abu Saleh da ke Khan Yunis a Gaza ranar 7 ga Disamba. Hoto: AAMazauna yankin da kungiyoyin kare fararen hula sun ceto wani yaro Bafalasdine a karkashin baraguzan gini bayan harin da Isra'ila ta kai kan wani gidan Abu Saleh da ke Khan Yunis a Gaza ranar 7 ga Disamba. Hoto: AA

2300 GMT — Amurka ta ce akwai bukatar Isra'ila ta kara yin kokarin kare Falasdinawa fararen hula

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce akwai “tazara” tsakanin abin da Isra’ila ta yi alkawarin yi na kare Falasdinawa fararen hula da sakamakon da aka samu kawo yanzu tun lokacin da ta fara kai hare-hare masu tsanani da kuma mamaye Gaza.

Blinken ya ce ya zama wajibi Isra'ila ta kara yin kokarin ganin ba a kashe ko jikkata fararen hula ba.

Ya tuna cewa jami'an Isra'ila sun ba shi tabbaci a ziyarar da ya kai Isra'ila a makon da ya gabata cewa "za su kara yin taka tsantsan don kare rayukan fararen hula." Ya ce ya sake tayar da batun a ranar Alhamis.

"Yayin da muke tsaye a nan kusan mako guda a cikin wannan yakin a kudancin kuma bayan kawo karshen tsagaita wuta, ya zama wajibi, ya zama wajibi, cewa Isra'ila ta ba da kariya ga fararen hula," Blinken ya fada a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Washington tare da sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameron da ke ziyara.

"Kuma akwai sauran tazara tsakanin ainihin abin da na fada lokacin da nake can tsakanin aniyar kare fararen hula da hakikanin sakamakon da muke gani a kasa," in ji shi.

#