Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 405 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,712 da jikkata 103,258, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,365 tun Oktoban bara.
Alhamis, 14 ga Nuwamban 2024
1114 GMT –– Hanyoyin yakin Isra'ila a Gaza daidai suke da kisan kare dangi, ciki har da kisan fararen hula da ake yi da kuma wahalar da Falasdinawa da ake yi, in ji Kwamitin Musamman na Majalisar Dinkin Duniya.
Karin bayani ????
0735 GMT — An kai hari kudancin Beirut bayan umarnin kwashe mutane na Isra'ila - Rahoto
Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya afka wa yankunan kudancin babban birnin kasar Labanon bayan da Isra'ila ta gargadi mazauna yankin da su fice daga wani bangare na sansanin Hezbollah, kamar yadda hotunan AFP suka nuna.
Wani hayaki mai launin toka ya turnuƙe yankin bayan harin na baya-bayan nan tun bayan da Isra'ila ta tsananta kai hare-haren bam a Lebanon a watan Satumba.
Jim kadan gabanin harin, Isra’ila ta yi gargadi ga mazauna yankin da su bar gidajensu.
0745 GMT — Isra'ila ta kai harin bam a birnin Gaza, inda ta kashe Falasdinawa da dama
Harin bama-bamai da Isra'ila ta kai a unguwar Sheikh Radwan da ke birnin Gaza inda fararen hula ke zaune, ya kashe Falasdinawa akalla uku.
A wani hari na daban da aka kai a wajen makarantar Hamama, Isra'ila ta raunata Falasdinawa 10, in ji cibiyar yada labarai ta Falasdinu (PIC).
Har ila yau Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a duk fadin Gaza, inda aka harba makaman atilari a yankunan kudanci da gabashin unguwar Zeitoun.