Isra'ila ta kwashe kwana 38 tana luguden wuta a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 11,100, ciki har da mata da kananan yara fiye da 8,000, tun bayan da Hamas ta kai mata harin ba-zata ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Hamas ta yi kira a sa baki don shigar da fetur asibitocin Gaza

0025 GMT Netanyahu ya nuna alamar tattaunawa da Hamas don sako wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya nuna alamun cewa za a kulla yarjejeniya da kungiyar Hamas domin yiwuwar sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

"Ina ganin idan ban yi magana sosai a kan batun ba, za a fi samun damar tabbatar da aukuwarsa," a cewar Netanyahu a hira da kafar watsa labaran Amurka ta NBC News.

Da yake bayar da amsa kan ko ya san inda mutanen da aka yi garkuwa da su suke a halin yanzu, sai Netanyahu ya ce: "Mun san abubuwa da dama, amma ba na so na yi magana fiye da hakan".

Firaiministan Isra'ila ya kara da cewa dole ne duk wata yarjejeniya ta kasance tana kunshe da "tursasawa, wato tursasawa irin ta sojoji".

0000 GMT — Hamas ta yi kira a sa baki don shigar da fetur asibitocin Gaza

Kungiyar fafutukar kare hakkin Falasdinawa ta Hamas ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniya su "gaggauta sanya baki don kawo fetur Gaza yadda asibitoci za su ci gaba da aiki.”

Ta fitar da sanarwa domin martani ga ikirarin da sojojin Isra'ila suka yi cewa ta ki karbar fetur domin amfani da shi a Asibitin Al Shifa da ke Gaza.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila Avichay Adraee ranar Lahadi ya wallafa sako a shafin X da ke cewa sun bayar da lita 300 na fetur ga Asibitin Al Shifa amma Hamas ta hana jami'an asibitin karba. Sai dai Hamas ta bayyana wannan kalami a matsayin "karya."

“Hamas ba ta cikin masu gudanar da Asibitin Al Shifa, sannan ba ta cikin asibitin, kana Asibitin yana karkashin kulawar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu, wadda ke tafiyar da ayyukansa na gudanarwa da na yau da kullum,” in ji kungiyar.

#