Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 88 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 21,978 da jikkata 56,697a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira.
2335 GMT —Hamas ta nemi ICRC ta dauki mataki kan dokokin da Isra'ila ta karya na kare 'yancin Falasdinawa fursunoni
Kungiyar Hamas da ke fafutukar kare mutuncin Falasdinawa ta yi kira ga kungiyar agaji ta International Committee of the Red Cross [ICRC] da ta tattara irin dokokin kara hakkin dan'adam na Falasdinawan da ke tsare a gidajen yari da Isra'ila ta karya, musamman yadda take gallaza wa mata.
A wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta bukaci ICRC da sauran kungiyoyin kare hakkin dan'adam "su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na daukar mataki kan cin zali da take 'yanci da Isra'ila ke yi wa mata Falasdinawa wadanda ke tsare a gidajen yarinta."
Sanarwar ta kara da cewsa "Matan Falasdinawa da ke tsare a gidajen yari suna fuskantar tsananin rashin abinci da hana su magunguna."
Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa Falasdinawa sama da 7,800 ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, ciki har da mata 80.
2140 GMT —Kotun Kolin Isra'ila ta yi watsi da shirin Netanyahu na rage ikon alkalai
Kotun Kolin Isra'ila ta yi watsi da wani muhimmin bangare na shirin Firaiminista Benjamin Netanyahu na yin garambawul da zai rage karfin iko ga fannin shari'a na kasar.
Alkalai takwas ne suka yi watsi da kudirin yayin da bakwai suka goyi bayansa.
Kudurin, wanda Majalisar Dokokin kasar ta amince da shi a watan Yulin da ya gabata, ya soke ikon da Kotun Koli take da shi na ayyana matakan da gwamnati ta dauka a matsayin marasa kan gado sannan ya rage karfin ikon alkalai.
Majalisar Dokokin Isra'ila mai suna Knesset ta yi kudirin kwaskwarima ranar 24 ga watan Yuli, sannan ta amince da shi.
Sai dai gamayyar jam'iyyun da ke mulkin kasar ta yi fatali da hukuncin na ranar Litinin, inda Ministan Shari'a Yariv Levin ya ce hakan nuna kyama ne ga "hadin kai" da ake bukata a lokacin yaki.
Jam'iyyun hamayya a kasar sun goyi bayan hukuncin, inda shugaban jam'iyyar adawa Yair Lapid ya ce yana mara wa kotun cikakken baya "a rawar da take takawa wajen kare al'ummar Isra'ila."