Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 42 tana kaiwa a Gaza ta sama da ta kasa  sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 11,500, fiye da 4,700 daga cikinsu kananan yara.

KAI-TSAYE: Hamas ta ce ta shirya gwabza yaki mai tsawo da Isra'ila

0625 GMT — Hamas ta ce ta shirya gwabza yaki mai tsawo da Isra'ila

Shugaban bangaren siyasa na Hamas ya ce kungiyar da ke Zirin Gaza ta shirta tsaf domin gwabza yaki na tsawon lokaci da sojojin Isra'ila.

A wani jawabi da aka nada kuma ya gabatar ranar Alhamis, Ismail Haniyeh ya jinjina wa Falasdinawa da kuma yadda suka hada kai wajen “wargaza sojojin Isra'ila da rage musu karfi ta kowacce fuska.”

“Idan har makiya suna so a yi yaki mai tsawo, karfinmu ya fi na makiyanmu kuma bijirewarmu ba za ta gushe ba,” yana mai nuna cewa “mayakanmu suna fafatawa a yaki da makiyanmu Yahudawa kuma za mu yi nasara,” a cewar Haniyeh.

Ya bayyana irin “nasarorin da mambobinmu suka samu a Zirin Gaza,” yana mai karawa da cewa “gwarazanmu suna fitar da mu kunya a Gaza, suna jajircewa da kuma cin galaba a kan makiyanmu da lalata ababen hawansu.”

“Duniya za ta ga lokacin da Rundunar Al-Qassam da masu taya ta aiki za su murkushe mamayar da Isra'ila ke yi a Gaza, kamar yadda suka yi shekara 18 da suka gabata.”

Haniyeh duniya za ta ga lokacin da Rundunar Al-Qassam da masu taya ta aiki za su murkushe mamayar da Isra'ila ke yi a Gaza./Hoto:AA

0550 GMT — Dubban mutane a Asibitin Al Shifa na 'kokarin kauce wa mutuwa'

Mutum fiye da 7,000 da suka hada da wadanda aka kora daga gidajensu da marasa lafiya da jami'an kiwon lafiya a Asibitin Al Shifa suna "kokarin kauce wa mutuwa sakamakon rashin ruwa da abinci" saboda kawanyar da dakarun Isra'ila suka yi musu, kamar yadda ofishin watsa labarai na Gaza ya bayyana.

A wata sanarwa da ofishin ya wallafa a manhajar Telegram, ya jaddada irin mawuyacin halin da mutanen suke ciki, yana mai bayyana cewa "babu abinci da ruwa da madarar da za a bai wa jarirai a Asibitin Al Shifa."

"Bakwaini da ke fama da rashin abinci za su iya rasuwa a asibitin saboda rashin wutar lantarki, abin da ya sa aka fitar da su daga kwalaben da suke ciki," in ji sanarwar.

Amurka tana so a kare mutanen Gaza kuma ba ta so a ci gaba da kai hari asibitoci, a cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar. / Hoto: Reuters

Ofishin ya bayyana "mawuyacin halin da ake ciki a Asibitin Al Shifa, inda mutum akalla 650 suke jiyya da kuma mutum 7,000 da aka kora daga gidajensu suke samun mafaka."

Ma'aikatan kiwon lafiya da majiyyata da mutanen da aka raba da gidajensu suna kokarin kauce wa mutuwa saboda rashin "abubuwan bukatu na rayuwa."

Sanarwar ta kara da cewa "dakarun Isra'ila sun lalata dukkan ababen hawa da ke cikin asibitin sannan sun hana ma'aikata da majiyyata fita daga cikinsa."

#