Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 322, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,265 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 93,144, kana an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000.
Juma'a, 23 ga watan Agusta, 2024
1159 GMT ––Wani babban jami'i a ƙungiyar Hamas ya soki firaministan Isra'ila a kan ƙin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yana mai cewa zaman dakarun Isra'ila a kan iyakar Masar na cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta.
Tawagar Isra'ila ta je Alƙahira "domin tattaunawa kan sako mutanen da aka yi garkuwa da su", in ji Omer Dostri, mai magana da yawun Benjamin Netanyahu a hira da AFP.
Sai dai wakilan Hamas ba sa cikin tattaunawar kuma babban jami'in ƙungiyar, Osama Badran, ya shaida wa AFP cewa dagewar da Netanyahu ta ci gaba da kasancewar dakarunsu a yankin Philadelphi na an iyaka ta nuna "ƙin yarda a kammala yarjejeniyar tsagaita wuta".
Egypt with fellow mediators Qatar and the United States have for months tried to reach a deal to end more than 10 months of Israeli war on Palestinians in Gaza.
0507 GMT –– Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu, ciki har da wani yaro a hare-hare biyu ta sama da jiragen yaƙinta suka kai kan tarukan fararen-hula a kudancin Gaza da tsakar dare. Kazalika gomman mutane sun jikkata.
Likitoci a Asibitin Nasser sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (WAFA) cewa an kai musu gawawwakin mutum uku, ciki har da wani yaro, bayan harin da Isra'ila ta kai a garin Abasan.
Bugu da ƙari, jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a yankin Zaytoun a Birnin Gaza inda suka kashe mutum ɗaya tare da jikkata da dama.
0341 GMT — Harris ta yi alƙawarin 'aiwatar' da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Kamala Harris ta yi alƙawarin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sannan ta ce idan ta zama shugabar Amurka ba za ta "ɗasa" da masu mulkin kama-karya kamar yadda Donald Trump na jam'iyyar Republican ya yi ba.
"Yanzu lokaci ya yi da za a kammala yarjejeniyar sako mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta," kamar yadda mataimakiyar shugaban ta Amurka ta shaida wa magoya bayanta a taron Democratic National Convention a yayin da ta amince da tsayar da ita takarar shugaban ƙasa.