Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Gomman gawawwaki sun isa asibitocin Indonesia da Kamal Adwan da ke Gaza

1230 GMT — Gomman gawawwaki sun isa asibitocin Indonesia da Kamal Adwan da ke Gaza

Gomman gawawwaki sun isa asibitocin Indonesia da Kamal Adwan da ke Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu da ke Gaza ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

“Wasu karin gawawwaki shida sun sake isowa Asibitin Al Aqsa sakamakon harin da masu mamaya suka kai gidan Aqtifan da ke Deir Al Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

0850 GMT — Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta ce ta kakkabo jirgin Isra’ila maras matuki da makami mai linzami a yankin Galilee Panhandle.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar da safe inda ta ce ta harba makamin nata da misalin karfe 1:45 agogon kasar, (23:45 agogon GMT).

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare Zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba. /Hoto:Reuters

Ta bayyana cewa ta hango lokacin da tarwatsatsun sassan jirgin ke fadawa a yankin Galilee Panhandle.

Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da sanarwa domin gasgatawa ko kuma karyata ikirarin na Hezbollah ba.

Sama da Falasdinawa 12,000 Isra’ila ta kashe zuwa yanzu, inda sama da 8,300 yara ne da mata, haka kuma ta raunata sama da 30,000.

#