Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 54 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara. Kimanin mutum 7,000 aka danne a baraguzan gine-gine wadanda Isra'ila ta yi wa luguden wuta, a cewar hukumomi.
0657 GMT — Gaza tana fuskantar tsananin karancin abinci – World Food Programme
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya wato World Food Programme (WFP) ya yi gargadi cewa akwai yiwuwar Gaza ya yi fama da matsanancin karancin abinci, yana mai jaddada cewa abincin da ake kai wa bai isa ba wurin magance matasalar yunwa a yankin.
"Akwai matukar yiwuwar mutanen Gaza, musamman mata da kananan yara, za su fuskanci matukar karancin abinci idan Shirin WFP bai ci gaba da samar da abinci ba," in ji wata sanarwa da Shirin na WFP ya fitar.
" WFP na matukar bukatar abincin da zai bai wa fiye da mutum 120,000 a Gaza a matakin farko," a cewar sanarwar.
Samer Abdeljaber, wakilin WFP kuma darakta a yankin Falasdinu, ya ce tawagarsa ta ga yadda mutane suke cikin "yunwa da bala'i da rushewar muhallansu" kuma ba su samu agaji ko daya ba cikin makonnin da suka gabata.
0230 GMT — Kungiyar Hamas ta gayyaci Elon Musk zuwa Gaza don ya ga barnar da Isra'ila ta yi
Wani babban jami'in Hamas ya gayyaci hamshakin mai arzikin nan na Amurka Elon Musk zuwa yankin Gaza da aka yi wa kawanya don ya ga girman barnar da hare-haren Isra'ila suka jawo da yadda hakan ya yi asarar rayukan Falasdinawa 15,000, mafi yawansu mata da yara.
"Muna gayyatarsa [Elon Musk] ya ziyarci Gaza don ganin girman kisan kiyashi da halakar da aka yi wa al'ummar Gaza, tare da bin ka'idodin haƙiƙa da gaskiya," kamar yadda babban jami'in Hamas Osama Hamdan ya fada a wani taron manema labarai a birnin Beirut ranar Talata.
A ranar Litinin ne ma'abota shafukan sada zumunta suka dirar wa attajiri Elon Musk saboda nuna goyon baya ga wani sako da aka wallafa na nuna kyamar Yahudawa, yana zagaya wurin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra’ila harin ba-zata tare da bayyana aniyarsa ta yin duk abin da ya dace domin daƙile yaɗuwar ƙyama.
2206 GMT — CIA, Mossad, Qatar suna tattaunawa don tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza - Kafofin yada labaran Isra'ila
Kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra'ila KAN ta rawaito cewa an fara tattaunawa a kasar Qatar kan wata sabuwar yarjejeniya ta tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Gaza da Isra'ila ta yi wa ƙawanya.
KAN ta ce dakatarwar za ta hada da sakin dukkan fursunonin Isra'ila a Gaza da aka yi wa ƙawanya, ciki har da sojoji, da kuma sakin Falasdinawan da Isra'ila take tsare da su a gidajen yari, har da wasu da aka samu da laifin kisan 'yan Isra'ila.
Falasdinawa a ko da yaushe suna yin watsi da tuhumar da gwamnatin 'yan mamaya da kotuna ke yi musu.
KAN ta ce kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana amincewarta da fadada abin da sabuwar yarjejeniyar za ta ƙunsa amma ta kara da cewa ta bukaci da a tsagaita wuta, wanda har yanzu Isra'ila ta ƙi amincewa da shi.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa, shugaban hukumar leken asirin Isra'ila Mossad, David Barnea da shugaban hukumar leken asirin Amurka (CIA) William Burns, da daraktan hukumar leken asirin Masar (GIS) Abbas Kamel da firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani ne suke halartar tattaunawar.