Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 136 — inda zuwa yanzu ya kashe aƙalla Falasɗinawa 28,985 tare da jikkata wasu 68,883.

KAI-TSAYE: Falasɗinu za ta bayar da shaida a gaban Kotun Duniya

1053 GMT — Falasɗinu za ta bayar da shaida a gaban Kotun Duniya

Ƙasar Palestine za ta zama ƙasa ta farko cikin ƙasashe 52 da za su yi magana a Kotun Duniya yayin da kotun za ta shafe kwana shida tana sauraren ƙarar da aka shigar a gabanta.

“Muna so mu ji sabbin kalamai daga kotun” in ji Omar Awadallah, shugaban sashen Majalisar Ɗinkin Duniya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasɗinu, gabannin soma sauraren ƙarar.

“Akwai buƙatar su yi la’akari da batun kisan kiyashi a koken Afirka ta Kudu,” kamar yadda ya bayyana inda yake bayani dangane da wani koken na daban da ke gaban kotum. “A yanzu muna so su yi la’akari da batun wariyar launin fata.”

0150 GMT — Isra'ila ta dage kan kai hari Gaza da 'nufin korar mutane ƙarfi da yaji'

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce Isra'ila ta dage kan ci gaba da kai hare-hare a Gaza domin korar mutane da raba su da muhallansu, musamman a birnin Rafah.

"Gwamnatin Isra'ila da sojojinta na ci gaba da kai hare-hare a garuruwa daban-daban na Gaza, musamman Rafah da nufin korar 'yan ƙasar ta ƙarfi da yaji. Ba za mu amince da hakan ba, haka kuma 'yan'uwanmu da ma duniya baki daya ba za su amince ba," ya faɗa a wani taro na gwamnatin Falasdinu da aka gudanar a Ramallah, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA.

Ya jaddada cewa halin da ake ciki a Rafah ya zama mai matuƙar haɗari da wahala, yana bukatar gwamnatin Falasdinu ta dauki matakin gaggawa.

Ya kara da cewa sun hallara ne domin tattaunawa kan lamarin domin hana ci gaba da kai hare-hare da kuma hana Isra'ila korar Falasdinawa daga yankunansu da kuma kasarsu.

0133 GMT WHO ta taimaka wajen kwashe marasa lafiya 14 daga Asibitin Nasser da ke Gaza da aka yi wa ƙawanya

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta taimaka wajen kwashe majinyata 14 daga Asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza, wanda sojojin Isra'ila ke yi wa ƙawanya, in ji Ma'aikatar Lafiya ta Gaza.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce an kai marasa lafiyan, wadanda suka hada da biyar da aka yi wa wankin ƙoda da uku da ke cikin tsananin kulawa, zuwa asibitocin da ke kudancin kasar, sakamakon kokarin da hukumar ta WHO ta yi.

Ta ce ana ci gaba da matsa lamba kan Isra'ila ta kwashe dukkan majinyata daga asibitin, wanda ta mayar da shi barikin soji bayan katse wutar lantarki da kuma hana na'urorin iskar oxygen aiki.

#