Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 145 - ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 29,878, galibi yara da mata, tare da jikkata mutum 70,215.

KAI-TSAYE: Falasɗinu ta bukaci Isra'ila ta biya kuɗin sake gina Gaza

2245 GMT — Falasɗinu ta bukaci Isra'ila ta biya kuɗin sake gina Gaza

Hukumomin Falasɗinu sun buƙaci Isra'ila ta ɗauki nauyin biyan kuɗin sake gina Gaza da kuma nuna babbar himma wajen tabbatar da sulhu tsakanin kasashen biyu.

Firaiminista Muhammad Shtayyeh ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da Ministan Harkokin Wajen Japan Tsuji Kiyoto a birnin Ramallah, inda ya ce: "Dole ne a ɗora wa Isra'ila alhakin ɓarnar da aka yi a Zirin Gaza da kuma ɗaukar nauyin sake gina ta."

Gwamnatin Shtayyeh za ta yi aiki a matsayin gwamnatin riƙon ƙwarya har sai an kafa sabuwar gwamnati, bayan da ya yi murabus a ranar Litinin.

Shtayyeh ya kuma yi Allah wadai da matakin na Isra'ila, yana mai cewa "tana aiwatar da mummunan zalunci kan al'ummar Falasɗinu, tana ƙarfafa wariyar launin fata da kuma nuna kamar ba za ta fuskanci wani sakamako na shari'a ba."

Ya jaddada cewa, babban abin da ya sa a gaba shi ne dakatar da kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummarmu a Zirin Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Birnin Ƙudus, da kuma ƙara buɗe mashigar Zirin Gaza domin ba da damar taimakon jinƙai da na lafiya cikin gaggawa.

Shtayyeh ya kuma bayar da shawarar "ƙara yin ƙoƙarin kiyaye hanyar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu da aiwatar da ƙudurin cimma hakan ta hanyar kawo ƙarshen mamayar da kuma amincewa da ƙasar Falasɗinu kamar yadda yake a cikin dokokin 1967 da sany Ƙudus a matsayin babban birninta."

2200 GMT — Amurka ta ce Isra'ila ba ta gabatar da shirin kare fararen hula ba ta kutsa Rafah

Fadar White House ta ce ba a gabatar wa Amurka da wani shirin Isra'ila na kare lafiyar fararen hula a Gaza ba idan har sojoji suka kutsa Rafah don fara kai hare-hare.

"Ba a gabatar mana da wani tsari ko ɗaya ba. Ba zan iya magana ga yawun Isra'ilawa ba ko kuma matakin da shirinsu ya kai ko kuma yadda hakan zai kasance ba," in ji kakakin Kwamitin Tsaron Amurka John Kirby a wani taron manema labarai.

Isra'ila na shirin fadada hare-hare ta kasa zuwa Rafah, birnin da ke kudancin Gaza da ke kan iyaka da Masar, kuma mahaifar Falasdinawa miliyan ɗaya da dubu 400 ne, a daidai lokacin da kasashen duniya ke gargadin illar da hakan zai haifar.

Kirby ya yi nuni da cewa, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya ɗora wa janar-janar ɗinsa aikin samar da wani shiri.

#