Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 180 tana kai wa Falasɗinawa da ke Gaza sun yin sanadin mutuwar aƙalla mutum 32,916 da jikkatar fiye da mutum 75,494 a yayin da ƙasashen duniya ke Allah wadarai da ita kan kashe ma'aikatan agaji a Gaza.

Kai-tsaye: Falasɗinawa sun sake bijiro da buƙatar neman kujerar mamba a MDD ana tsaka da yaƙin Isra'ila

2130 GMT — Falasɗinawa sun sake bijiro da buƙatar neman kujerar dindindin a MDD ana tsaka da yaƙin Isra'ila

A hukumance yankin Falasɗinu ya sake bijiro da buƙatar neman zama mamba na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, a cewar wata wasiƙa daga wakilinsu a MDD.

"Bayan na samu umarni daga shugabannin Falasɗinawa, ina sake miƙa buƙata ga Kwamitin Tsaro a watan Afrilu na 2024 don a ba mu matsayin mamba ta dindindin," in ji wasiƙar da Riyad Mansour ya aika wa Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, wadda aka miƙa wa Kwamitin Tsaro.

Falasɗinawa, waɗanda suke matsayi na ƴan-kallo tun shekarar 2012, sun kwashe shekaru da dama suna neman a ba su matsayin mamba na dindindin, lamarin da ke nufin a amince da yankin a matsayin ƙasa mai yancin kanta, kasancewa galibin ƙasashe mambobin majalisar sun yarda ta ita a matsayin ƙasa.

Masu sharhi na ganin zai yi wahala buƙatar ta Falasɗinu ta samu karɓuwa domin kuwa Amurka, babbar ƙawar Isra'ila, tana iya yin amfani da ƙarfinta a Kwamitin Tsaro don hawa kujerar na-ƙi.

Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Ƙungiyar Ƙasashe Musulmai da kuma Ƙungiyar Ƙasashe ƴan ba-ruwanmu sun aike da wasiƙa ga Sakatare Janar ma MDD ranar Talata, inda suka goyi bayan kasancewar Falasɗinu a matsayin mamba ta majalisar.

"Muna so mu jawo hankalinka cewa, a wannan ranar, mambobi 140 sun amince d kasancewar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴancin kanta," a cewar wasiƙar haɗin-gwiwa da ƙasashen suka aika wa shugaban majalisar.

0106 GMT — Isra'ila ta ce kisan da ta yi wa ma'aikatan agaji 'babban kuskure be'

Shugaban sojojin Isra'ila ya ce kisan da dakarunsu suka yi wa ma'aikatan agaji bakwai a Gaza "babban kuskure ne", bayan sun sha suka daga ƙasashen duniya.

"Wannan lamari babban kuskure ne," in ji shugaban sojojin Isra'ila Herzi Halevi a wanisaƙon bidiyo da ya fitar kan kisan da sojojinsu suka yi wa ma'aikatan World Central Kitchen (WCK) ranar Litinin.

"Bai kamata a ce hakan ya faru ba," a cewar Halevi, a yayin da ya ɗora alhakin kisan kan "kuskure -— wanda ya faru saboda an kai harin ne da daddare".

"Muna neman gafara ga mambobin WCK game da illar da muka yi ba tare da niyya ba."

#