Hare-haren da Isra'ila ta kwashe 68 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,412, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 50,100 sun jikkata kana dubban na binne a karkashin baraguzan gine-gine

KAI-TSAYE: EU ta bukaci a kakaba wa Isra'ilawa masu tsattsauran ra'ayi takunkumi

1445 EU ta bukaci da a kakaba takunkumi kan Isra'ilawa masu tsattsauran ra'ayi 'yan mamaya a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta goyi bayan ƙaƙaba takunkumi kan Isra'ilawa masu tsatsauran ra'ayi da ke kai hare-hare kan Falasdinawa a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan suka mamaye.

Shugabar ta EU ta fada wa 'yan majalisar Tarayyar Turai a ranar Laraba cewa "Tashe-tashen hankula da masu tsattsauran ra'ayi ke yi na janyo wa Falasdinawa wahalhalu. Hakan na kawo cikas ga fatan samun dauwamammen zaman lafiya kuma zai iya kara ta'azzara rashin zaman lafiya a yankin."

"Ina goyon bayan sanya takunkumi ga wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare a Yammacin Kogin Jordan. Dole ne a yi musu hisabi. Wannan tashin hankalin ba shi da alaka da yaki da Hamas don haka dole ne a daina."

Kalaman Von der Leyen na zuwa ne bayan da babban jami'in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya fada a ranar Litinin cewa, cewa zai gabatar da wata shawara ta sanya takunkumi ga mazauna Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye.

Matakan za su bukaci goyon bayan baki daya daga kasashe mambobin kungiyar EU 27, amma akwai rarrabuwar kawuna a cikin kungiyar.

1430 Allurar rigakafi ta yara ta ƙare a Gaza

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce ta ƙarar da dukkan alluran rigakafin yara tare da yin gargadin "lalacewar tsarin kiwon lafiya."

Sanarwar ta zo ne a lokacin da aka shafe fiye da wata biyu da fara yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, a daidai lokacin da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi gargadi game da mummunan yanayi a yankin Falasdinu mai cunkoson jama'a.

Jami'in kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a yankunan Falasdinu, Lynn Hastings, ya ce UNICEF na duba lamarin.

Hastings ya shaida wa manema labarai a wani taron tattaunawa ta ntanet cewa, "Alurar rigakafi na daya daga cikin muhimman abubuwan da muke kokarin kawowa don tabbatar da cewa mun sami damar ci gaba da wayar da kai kan muhimmancinsu."

Tedros Ghebreyesus, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, ya yi gargadi a ranar Lahadin da ta gabata cewa "Tsarin kiwon lafiya na Gaza yana durkushewa," inda asibitoci 14 kawai cikin 36 ke aiki, kuma ana fama da ƙarancin kayayyakin aiki.

Ana sa ran hadarin zai kara tsananta tare da tabarbarewar yanayi da kuma gabatowar yanayin hunturu," in ji shi.

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta yi kira ga cibiyoyin kasa da kasa da su samar da allurar rigakafin da ake bukata cikin gaggawa "don hana aukuwar bala'i".

1320 — Isra’ila ta ce an raunata sojojinta 619 a kasa da wata biyu

Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin dakarun Isra'ila da kuma na Hamas. / Hoto: Reuters

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da cewa akwai dakarunta 19 da suka samu rauni a yakin da take yi a Gaza a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce adadin sojojinta da Isra’ilar ta raunata tun bayan da Isra’ilar ta soma kai hari ta kasa a Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba sun kai 619.

Ta bayyana cewa daga cikin sojojin nata da aka raunata, akwai wasu 139 da ke cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

1240 GMT — Dakarun Hamas sun ce sun yi wa sojojin Isra'ila 15 kwanton-bauna

Dakarun Hamas sun bayyana cewa sun yi wa sojojin Isra’ila 15 kwanton bauna, kamar yadda suka bayyana a wata sanarwa.

Duk da sanarwar ba ta yi karin bayani kan sojojin da suka jikkata ba, amma ta tabbatar da cewa akwai wasu da suka rasa ransu.

Wannan na zuwa ne bayan sojojin na Isra’ila a safiyar Laraba sun sanar da cewa an kashe musu mutum goma a Gaza a cikin sa’o’i 24.

Sojojin na Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa a Gaza. / Hoto: Reuters

0715 GMT — Isra'ila ta ce an kashe karin sojojinta 10 a arewacin Gaza

Rundunar sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da cewa an kashe karin sojojinta goma, ciki har da kwamandoji a arewacin Gaza a sa’o’i 24 da suka gabata.

Tun da farko rundunar ta sanar da cewa takwas ne aka kashe, amma daga baya rundunar sojin ta sake fitar da wata sanarwa inda ta ce akwai karin sojoji biyu wadanda aka kashe.

Kafar watsa labarai ta Isra’ila KAN ta sanar da cewa daga cikin sojojin na Isra’ila da aka kashe har da Laftanar Kanal Tomer Grinberg mai shekara 35 da Manjo Moshe Avram da Roei Meldasi mai shekara 23 wadanda duka kwamandoji ne.

0023 GMT — Australia ta goyi bayan kudurin MDD na tsagaita wuta a Gaza a ra'ayin da ya sha bamban da Amurka

Ministar harkokin wajen Australia Penny Wong, ta ce kasar ta goyi bayan wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita wuta a Zirin Gaza, saboda nuna damuwa ga fararen hula a yankin da aka yi wa ƙawanya, a wani ra'ayi da ya jawo rabuwar kai da babbar ƙawarta Amurka.

Bayan gargadin da jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka yi game da ta'azzarar ƙazamin rikicin jinƙai a Gaza a yakin da Isra'ila ta kwashe watanni biyu ana yi a can, MDD mai wakilai 193 ta amince da ƙudurin tsagaita wuta inda ƙasashe 153 da suka hada da Australia suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsagaita wutar, inda 23 kuma suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri'ar.

Kasashe goma ne suka kada kuri'ar ƙin amincewa da tsagaita wutar kuma sun haɗa da Amurka da Isra'ila.

Wong ya shaida wa wani taron manema labarai a Adelaide bayan da MDD ta zartar da kudurin cewa, Australia ta ci gaba da tabbatar da hakkin Isra'ila na kare kanta. "Kuma a yin haka, mun ce dole ne Isra'ila ta mutunta dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, dole ne a kare fararen hula da kayayyakin aikin farar hula, ciki har da asibitoci.

"Kudurin da muka goyi bayan ya yi daidai da matsayin da muka zayyana a baya kan wadannan batutuwa."

0153 GMT — Jajircewar Falasɗinawa ta sa Biden ya gane yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza "hauka ne" : Hamas

Juriya da tsayin daka na al'ummar Falasdinu ya sa shugaban Amurka Joe Biden ya fahimci "haukar" sojojin Isra'ila a mamayar da suke yi a Gaza, in ji wani babban shugaba a Hamas.

Osama Hamdan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a birnin Beirut a lokacin da aka tambaye shi game da wani sharhi da kamfanin Biden ya yi a safiyar ranar cewa Isra'ila na rasa goyon bayanta a duniya.

Harin na Isra'ila "zai haifar da mummunan sakamako" kan Isra'ila da kuma yiwuwar sake zaben Biden, in ji shi.

Ya yi nuni da cewa akwai saɓani ƙarara a cikin kalaman na Biden, yana mai cewa a jiya ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga Isra'ila kuma a yau ya bayyana cewa Isra'ila ta fara rasa goyon bayan kasashen duniya.

Biden ya ce gwamnatin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na rasa goyon bayanta a duniya kuma "dole ne Netanyahu ya ƙarfafa tare da sauya" gwamnati don "nemo mafita ta dogon lokaci kan rikicin Isra'ila da Falasdinu."

#