Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma'aikatar lafiya

1220 GMT Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma'aikatar lafiya

Duka asbitoci a arewacin Gaza sun daina aiki, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.

Ma’aikatar ta bayyana cewa a halin yanzu ana kokarin fitar da marasa lafiya da ke Asibitin Indonesia.

A bangare guda kuma ma’aikatar ta bayyana cewa akwai mutum 259 wadanda aka raunata, da farar hula da dama a cikin Asibitin Al Shifa kuma babu ranar kwashe su.

0920 GMT — Hezbollah ta dauki nauyin kai wani hari kan Isra'ila

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta dauki nauyin wani hari da aka kai kan wasu gidajen da sojojin Isra’ila ke zama a Metulla da ke arewacin Isra’ila.

Hezbollah ta bayyana cewa ta kai wannan harin ne domin ramuwar gayya kan gidajen kai iyaka da Isra’ilar ta kai wa hari a kudancin Lebanon.

Kungiyar Hezbollah ta Yemen na taya Hamas yakin da take yi da Isra'ila. / Hoto: AA

A ‘yan kwanakin nan, Hezbollah ta kara yawan hare-haren da take kaiwa kan sojojin Isra’ila a kan iyaka, inda take kai hare-hare kusan goma a rana.

0715 GMT Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa 20 a sansanin 'yan gudun hijira

Akalla Falasdinawa 20 Isra'ila ta kara kashewa a hare-haren da ta kai gidaje biyu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Gaza ta bayyana.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ilar ke ci gaba da kai hare-hare kan gidaje da asibitoci a Gaza.

Zuwa yanzu akalla mutum 13,000 Isra'ilar ta kashe wadanda akasarinsu yara ne kanana da mata.

0640 GMT — Isra'ila ta rusa masallatai 83 a Falasdinu

Akalla masallatai 83 Isra’ila ta rusa baki daya a hare-haren da take kaiwa cikin Falasdinu tun daga 7 ga watan Oktoba, inda ta kuma lalata 170, kamar yadda kafar watsa labarai ta gwamnatin Gaza ta bayyana.

Falasdinawa sun zargi Isra’ila da kai hari masallatai a Gaza da gangan domin lalata su.

Baya ga masallatai, Isra'ilar ta kai hari asibitoci da coci-coci da makarantu. / Hoto:Reuters

Sai dai a nata bangaren Isra’ilar ta zargi dakarun na Hamas da amfani da masallatai a matsayin mafaka don guje wa hare-harensu.

0332 GMT — Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila a Gaza

Shugaban Hamas Isma'il Haniyeh ya ce ƙungiyar gwagwarmayarsa na gab da cimma yarjejeniyar sulhu da Isra'ila, a cewar wata sanarwa da aka wallafa ta kafar Telegram.

"Ana gab da cimma yarjejeniya kan sulhu," in ji Haniyeh, a cewar sanarwar

Masu shiga tsakani sun yi ta ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya don ba da damar sakin kusan fursunoni 240 da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, a lokacin harin da aka kai wa Isra'ila mafi muni a tarihinta.

Mayakan Hamas sun kuma kashe mutum kusan 1,200 a harin da suka kai kan iyaka.

Isra'ila ta kaddamar da hare-haren bama-bamai ba tare da bata lokaci ba tare da kai farmaki ta kasa a matsayin ramuwar gayya kan harin, inda ta lashi takobin rusa Hamas tare da ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

0117 GMT — Jami'in WHO ya ce halin da asibitin Gaza ke ciki ya zama 'bala'i'

Wani babban jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya bayyana halin da ake ciki a asibiti a Gaza a matsayin "mummunan bala'i", yana mai cewa yawanci ba sa aiki kuma abin da ya rage zai iya durkushewa sakamakon dubban haihuwar da ake sa ran mata za su yi a wata mai zuwa.

Bayanin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne sa'o'i kadan bayan da wani hari da aka kai ya shafi hawa na biyu na wani asibiti a arewacin Gaza, inda ya kashe mutum 12, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da kuma wani ma'aikacin lafiya.

#