Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 42 tana kaiwa a Gaza ta sama da ta kasa  sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 11,500, fiye da 4,700 daga cikinsu kananan yara.

KAI-TSAYE: Dubban mutane a Asibitin Al Shifa na 'kokarin kauce wa mutuwa'

0550 GMT — Dubban mutane a Asibitin Al Shifa na 'kokarin kauce wa mutuwa'

Mutum fiye da 7,000 da suka hada da wadanda aka kora daga gidajensu da marasa lafiya da jami'an kiwon lafiya a Asibitin Al Shifa suna "kokarin kauce wa mutuwa sakamakon rashin ruwa da abinci" saboda kawanyar da dakarun Isra'ila suka yi musu, kamar yadda ofishin watsa labarai na Gaza ya bayyana.

A wata sanarwa da ofishin ya wallafa a manhajar Telegram, ya jaddada irin mawuyacin halin da mutanen suke ciki, yana mai bayyana cewa "babu abinci da ruwa da madarar da za a bai wa jarirai a Asibitin Al Shifa."

"Bakwaini da ke fama da rashin abinci za su iya rasuwa a asibitin saboda rashin wutar lantarki, abin da ya sa aka fitar da su daga kwalaben da suke ciki," in ji sanarwar.

Ofishin ya bayyana "mawuyacin halin da ake ciki a Asibitin Al Shifa, inda mutum akalla 650 suke jiyya da kuma mutum 7,000 da aka kora daga gidajensu suke samun mafaka."

Ma'aikatan kiwon lafiya da majiyyata da mutanen da aka raba da gidajensu suna kokarin kauce wa mutuwa saboda rashin "abubuwan bukatu na rayuwa."

Sanarwar ta kara da cewa "dakarun Isra'ila sun lalata dukkan ababen hawa da ke cikin asibitin sannan sun hana ma'aikata da majiyyata fita daga cikinsa."

#