Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 336, inda ta kashe aƙalla Falasɗinawa 40,878 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,454, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa.
Juma'a 6 ga watan Satumban 2024
0410 GMT — Sojojin Isra'ila sun janye daga birnin Jenin da kuma wani sansanin 'yan gudun hijira da ke can, bayan shafe kwanaki 10 na "tashin hankali", in ji kamfanin dillancin labarai na Falasdinu (WAFA).
An kashe mutum 21 a cikin birnin da sansanin, in ji ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a cikin wata sanarwa.
Wani shaida na Reuters ya ce sojojin Isra'ila sun yi ɓarna mai yawa a kan ababen more rayuwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin Facebook, ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta zargi Isra'ila da yin mummunar ɓarna a yankin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye kamar yadda ta yi a Gaza, kamar yadda aka gani a garuruwan Jenin da Tulkarem da kuma sansanonin 'yan gudun hijira da ke can.
0552 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan wani matashin Falasdinawa a Ramallah
Sojojin Isra'ila sun kai hari kan wani matashi a kauyen Deir Abu Mashal da ke arewacin Ramallah, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA.
An kai harin ne a kauyen Shuqba a wani shingen bincike na wucin gadi da sojojin Isra'ila suka kafa, kamar yadda majiyoyin kasar suka bayyana.
Harin da sojojin Isra'ila suka kai kan Bilal Rabah Dar Atta ya yi sanadiyar karya masa yatsunsa. Nan take aka kai shi wani asibiti domin yi masa magani.