Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
1310 GMT — China ta yi kira kan kasashen duniya su dakatar da 'bala'in' da ke faruwa a Gaza
China ta yi kira ga kasashen waje kan su fito su dakatar da Gaza da bala’in da ke faruwa a Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Falasdinu.
Martanin na Beijing na zuwa ne bayan dakarun Isra’ila sun kai hari kan motocin daukar marasa lafiya a ranar Juma’a, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta ruwaito.
1108 GMT — Isra'ila ta ce an sake kashe mata wani soja a Gaza
Sojojin Isra’ila a ranar Litinin sun ce an sake kashe musu soja guda a Zirin Gaza a lokacin da sojojin ke ci gaba da kai hare-hare ta kasa a can.
Wata sanarwa da sojojin suka fitar ta ce sojan yana daga cikin dakarun bataliya ta tara.
Isra’ilar ta ce zuwa yanzu sojojinta 30 aka kashe sannan 260 suka samu rauni tun bayan da ta fara kai hari ta kasa a Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba.
0830 GMT — Isra'ila ta kashe sama da mutum 200 a Gaza a cikin dare
Hare-haren Isra’ila sun kashe sama da mutum 200 a cikin dare a Gaza, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.
“Sama da mutum 200 aka bayar da rahoton sun yi shahada a kisan kiyashin da aka yi cikin dare” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa, inda ta ce mutanen a Gaza kadai aka kashe su da arewacin Gaza.
0730 GMT — Dakarun Isra'ila sun kama 'yar gwagwarmayar Falasdinawa Ahed Tamimi
Sojojin Isra’ila a ranar Litinin sun kama daya daga cikin masu gwagwarmaya a Gabar Yamma da Kogin Jordan wato Ahed Tamimi, kamar yadda mahaifiyarta ta tabbatar.
“An kama Ahed mai shekara 23 bayan kai samame a gidanmu,” kamar yadda mahaifiyarta Nariman Tamimi ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Ta bayyana cewa sojojin na Isra’ila sun gudanar da bincike a cikin gidan sannan kuma suka kwace wayoyin salula na iyalan gidan.
0715 GMT — An harba rokoki daga Gaza zuwa Tel Aviv
'Yan sandan Isra'ila sun ce an harba rokoki da dama daga Gaza zuwa birnin Tel Aviv da yankunan da ke makwabtaka da shi.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta ambato 'yan sanda suna cewa wani makamin roka ya fada a wan sarari a birnin Rishon Lezion nkusa da Tel Aviv.
Qassam Brigades, wato fannin soji na kungiyar Hamas, ya ce shi ne ya harba rokokin a Tel Aviv domin yin raddi kan kashe fararen-hula da Isra'ila ke yi a Gaza.
0600 GMT — Sarkin Jordan ya ce an wurga 'magunguna na bukatun gaggawa' a Gaza
Jiragen sojin saman Jordan sun wuwwurga magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitocin tafi-da-gidanka da ke yankin Gaza da aka mamaye, a cewar Sarki Abdullah II da safiyar Litinin.
"Sojojin samanmu marasa tsoro sun jefa magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitin wucin-gadi na Jordan da ke Gaza," in ji sarkin a sakon da ya wallafa a shafin X.
0534 GMT — Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta aika da jirgin ruwan nukiliya Gabas ta Tsakiya
Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta ce aika da jirgin ruwan nukiliya yankin Gabas ta Tsakiya.
“Ranar 5 ga watan Nuwamba, jirgin ruwa samfurin Ohio-class ya isa yankin da ke karkashi ikon Amurka,” in ji sanarwar da Cibiyar Tsare-Tsare ta Amurka (CENTCOM) ta wallafa a shafin X.
Amurka ta aika da jirage biyu yankin Gabas ta Tsakiya tun daga ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar da farmakin Operation Al Aqsa Flood a Isra'ila.
0400 GMT — Adadin mutanen da suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 9,770
Ma'aikatar Kiwon Lafiya a Gaza ta ce ya zuwa ranar Lahadi mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Zirin Gaza sun kai 9,770.
“Mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba sun kai 9,770, cikinsu har da kananan yara 4,800 da mata 2,550,” in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
Ta kara da cewa a cikin awa 24 da suka wuce Isra'ila ta kashe Falasdinawa 270.