Yaƙin Isra’ila a Zirin Gaza da aka mamaye ya shiga rana ta 250, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 37,164 — kaso 71 mata da yara da jarirai — ya jikkata mutane 84,832, sannan an yi amanna fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka ruguza.
0512 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya tafi Qatar, wadda ita ce babbar mai shiga tsakani a rikicin Isra'ila da Falasɗinu, bayan ƙungiyar Hamas ta yi martani mai armashi kan ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya game da tsagaita wuta a Gaza.
Blinken, wanda yake ziyarar aiki ta ƙasashe huɗu a Gabas ta Tsakiya, zai gana da manyan jami'ai na gwamnatin Qatar, ƙasar da ita ce ta gabatar da saƙo na martanin ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu wato Hamas ta bayar.
Hamas, wadda ta mayar da martani kan shawarar da Joe Biden ya bayar ranar 31 ga watan Mayu, ta nemi a yi gyaran fuska kan jadawalin tsagaita wuta tare da neman Isra'ila ta janye dakarunta baki ɗaya daga Gaza, a cewar wasu majiyoyi da ke da masaniya game da batun.
Biden ya yi kira ga Isra'ila ta janye daga "manyan yankunan da jama'a suka fi yawa" tare da tsagaita wuta ta mako shida, sannan a tsawaita batun tsagaitar wutar sannu a hankali.
2001 GMT — Amurka tana "nazari" kan martanin Hamas a hukumance ga shirin sulhu na baya-bayan nan a yankin Gaza da aka mamaye, a cewar Fadar White House.
Washington ta karɓi "martanin da Hamas ta miƙa wa Qatar da Masar kuma muna nazarinsa yanzu haka," kamar yadda Mai Magana da yawun Majalisar Tsaron Ƙasa John Kirby ya shaida wa 'yan jarida, yayin da ya ƙi ba da cikakken bayani kan abin da martanin ya ƙunsa.
Mai magana da yawun Hamas Jihad Taha ya ce martanin ya ƙunshi "yin kwaskwarima da za ta tabbatar da tsagaita wuta da janyewar Isra'ila da sake gina Gaza da kuma musayar fursunoni." Shi ma Taha bai yi ƙarin bayani ba.
Sai dai yayin da suke goyon bayan yarjejeniyar, jami'an Hamas sun bayyana damuwa kan ko Isra'ila za ta yi aiki da sharuɗan, musammanma tanadin kawo ƙarshen yaƙi na dindindin, da ficewar Isra'ila daga Gaza baki ɗaya inda za a sako gaba ɗaya mutanen da ƙungiyar ta fafutuka take garkuwa da su.
Duk da cewa Amurka ta ce Isra'ila ta karɓi tayin, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya nuna alamun baki-biyu, yana cewa Isra'ila ba za ta tsaya ba har sai ruguza Hamas.
2239 GMT — Hamas ta ambaci martaninta kan sulhu a matsayin na 'gaske ma cike fata'
Martanin Hamas ga ƙudurin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza "ya buɗe wata babbar hanya" ta cim ma yarjejeniya, a cewar wata mamba a ɓangaren Hamas na siyasa Izzat al-Risha.
Martanin ƙungiyar "na sanin ya kamata ne, na gaske sannan mai cike da fata," a cewar al-Rishaq a cikin wata sanarwa.