Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0700 — Isra'ila tana harba bama-bamai da kashe 'jarirai da mata da tsofaffi' a Gaza — Shugaban Faransa Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga Isra'ila ta daina harba bama-bamai kan fararen-hula a Gaza, yana mai cewa babu wata hujja ta yin haka.
A hira da BBC, Macron ya ce Isra'ila tana da ikon kare kanta bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, sai dai ya kara da cewa: "Ana harba bama-bamai da kashe wadannan jarirai da mata da tsofaffi. Babu wata hujja ta yin haka. Saboda haka muna kira ga Isra'ila ta daina."
0629 GMT — An zargi Isra'ila da 'kaddamar da yaki' a asibitocin Gaza masu cike da jama'a
Ana ci gaba da gumurzu a kusa da asibotocin Gaza masu cike da jama'a, inda jami'an Falasdinu suka ce Isra'ila tana jefa musu abubuwan fashewa da yin luguden wuta.
"Yanzu haka Isra'ila ta kaddamar da yaki a asibitocin Gaza," a cewar Mohammad Abu Selmeyah, daraktan Asibitin Al Shifa.
Daga bisani ya ce Isra'ila ta kashe mutum akalla 25 a makarantar Al-Buraq da ke Birnin Gaza, inda mutanen da ta rusa wa gidaje suke samun mafaka.
Jami'ai a Gaza sun ce Isra'ila ta harba rokoki a harabar Asibitin Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a yankin, da safiyar Juma'a, sannan ta lalata Asibitin Indonesia kuma an cinna wuta a cibiyar kula da masu ciwon kansa ta Asibitin Nasser Rantissi.