Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 305, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,623 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum sama da 91,469, yayin da fiye da mutum 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine

Kai-tsaye: An yi wa Haniyeh kisan gilla ne da zummar tsawaita yaƙin Gaza  — Abbas

Talata, 6 ga watan Agusta, 2024

2319 GMT — An yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh kisan gilla ne da zummar tsawaita yaƙin Gaza da kuma dagula tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin, a cewar shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas a hira da kamfanin dillancin labaran RIA na gwamnatin Rasha.

"Babu tantama cewa an yi wa Mr. Haniyeh kisan gilla ne domin tsawaita yaƙin da kuma faɗaɗa shi," in ji Abbas, kamar yadda RIA ya ambato shi yana bayyanawa.

"Kisan nasa zai yi mummunan tasiri a kan yarjejeniyar da ake ƙoƙarin ƙullawa ta tsagaita wuta da kuma janyewar dakarun Isra'ila daga Gaza."

2035 GMT — Amurka na neman a yi sulhu yayin da Iran ke shirin ramuwar gayya kan Isra'ila

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira ga Tehran da Tel Aviv su amince da tsagaita wuta Gaza domin "karya lagon yaƙin" da ke faruwa, a yayin da Iran take shirin yin ramuwar gayya kan Isra'ila.

"Ƙara aukawa cikin yaƙi ba zai yi wa kowa daɗi ba. Zai haddasa ƙarin yaƙi da tazoma da rashin tsaro. Yana da muhimmanci mu karya lagon wannan yaƙin ta hanyar amincewa da tsagaita wuta a Gaza," in ji Blinken a hira da manema labarai.

Blinken ya yi kiran ne a yayin da ake cikin zaman ɗarɗar kan yiwuwar hare-haren da Iran da ƙawayenta za su kai wa Isra'ila domin yin martani kan kisan shugaban Hamas da kwadandan Hezbollah a makonnin da suka gabata.

Shugaan Amurka Joe Biden, wanda ƙasarsa ta aike da jiragen ruwan yaƙi da manyan makakai yankin Gabas ta Tsakiya, yana shirin gudanar da taro mai muhimmanci da shugabannin tsaron ƙasarsa.

Shugaban sojojin Amurka da ke kula da Gabas ta Tsakiya, Janar Michael Kurilla, ya isa Isra'ila inda ya gana da shugaban rundunar sojin ƙasar Laftanar Janar Herzi Halevi domin tattaunawa kan shirin kare kansu, a cewar wata sanarwa da suka fitar.

Wannan hoton wanda aka ɗauka daga arewacin Isra'ila, kusa da kan iyaka da Lebanon, ya nuna yadda hayaƙi ya tirniƙe sararin samaniya bayan Isra'ila ta kai hari a yankin Wazzani na Lebanon ranar 5 ga watan Agusta, 2024. / Hoto: AFP

2123 GMT — An jikkata wasu jami'an Amurka a harin da aka kai Iraƙi

An jikkata jami'an Amurka da dama sakamakon wani harin roka da a sansaninsu da ke Iraƙi, a cewar kakakin ma'aikatar tsaron ƙasar.

"An kai harin da muke zargi na roka ne a yau a kan dakarun Amurka da abokan aikinsu a sansanin sojin sama na al-Asad da ke Iraƙi. Bayanan farko sun nuna cewa jami'an Amurka da dama sun jikkata," in ji shi.

Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin na sansanin Ain al-Assad.

#