Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
11:30 GMT — An sake yin 'luguden wuta' a Asibitin Al Shifa na Gaza — WHO
Mai magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce "ana ta yin luguden wuta" a Asibitin Al Shifa, tana mai karawa da cewa asibitoci 20 sun daina aiki a Gaza.
Tun da farko, gwamnatin Hamas da ke Gaza ta ce wani hari da Isra'ila ta kai a babban asibitin yankin ya yi sanadin mutuwar mutum 13.
"Mutum goma sha uku sun yi shahada sannan gommai sun jikkata sakamakon hari ta sama da Isra'ila ta kai ginin Asibitin Al-Shifa a yau" a tsakiyar Birnin Gaza, a cewar sanarwar da gwamnati ta fitar.
Da aka tambaye ta kan harin da aka kai a harabar asibitin, kakakin WHO Margaret Harris ta ce: "Ban samu cikakken bayani kan Al Shifa ba amma muna sane cewa ana yi masa luguden wuta".
Ta kara da cewa ana "fafatawa mai zafi" a yankin, tana mai bayyana abubuwan da abokan aikinta da ke yankin suka gaya mata.
09:00 GMT — Turkiyya ta aika da jirgin ruwa cike da kayyakin jinkai da na kiwon lafiya zuwa Gaza
Turkiyya ta aika da kusan tan 500 na kayayyakin jinkai da na kiwon lafiya zuwa Gaza inda jirgin ruwan ya nufi iyakar Masar.
A safiyar ranar Juma’a ne jirgin ruwan Turkiyya ya tashi daga lardin Izmir dauke da kayan agaji don kai wa Falasdinawa da ke yankin Gaza da aka yi wa kawanya.
An loda kayayyakin agajin da motocin daukar marasa lafiya a cikin jirgin ruwa mai dakon kaya da ya tsaya a tashar ruwan Alsancak ta Izmir da yammacin ranar Alhamis.
Daga nan jirgin ya tashi zuwa Al Arish na kasar Masar, kusa da iyakar Rafah ya kasar da ke tsallaken yankin da ke fama da rikici.
07:30 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Gaza — Jami'ai
Kungiyar Bayar da Agaji ga Falasdinawa 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta ce an kashe ma'aikatanta 99 tun lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba.
Kwamishina Janar na UNRWA Philippe Lazzarini ne ya bayyana haka a wurin taron Kasashen Duniya Don Samar Da Jinkai ga Fararen-Hulan Gaza da aka yi a Paris, babban birnin Faransa.
"Wata daya da ya gabata ya kasance mai matukar wahala ga UNRWA," in ji Lazzarini.
Ya ce "an kashe abokan aikina 99 maza da mata a Gaza. Wannan shi ne adadi mafi girma na ma'aikatan kungiyar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da aka kashe sakamakon rikici a kankanen lokaci."
05:30 GMT — Yakin Isra'ila a Gaza ya jefa Falasdinawan Gaza 'sama da 400,000' cikin talauci
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda tattalin arzikin Falasdinu yake rushewa bayan Israila ta kwashe fiye da wata daya tana yi wa Gaza luguden wuta tare da yi wa daukacin yakin kawanya.
Tattalin arzikin Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza ya fadi da kashi hudu cikin dari lamarin da ya jefa fiye da mutum 400,000 cikin talauci — abin da ba a taba gani ba a yakin Syria da na Ukraine, da ma yake-yaken da aka yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na yankin Gaza a baya.
Isra'ila ta lalata ko ta rusa akalla kashi 45 cikin dari na dukkan gidajen Gaza, a cewar wata kididdiga da Shirin Majalisar Dinkin Duniya na Ci-gaba UN Development Program da kuma na Tattali Arziki da Walwala a Yankin Asiya wato UN Economic and Social Commission for West Asia suka fitar.