Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yin sanadin mutuwa Falasdinawa akalla 22,185 da jikkata mutum 57,035 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin.

KAI-TSAYE: An ji karar fashewar wasu abubuwa a kusa da jirgin ruwa a gabar tekun Yemen a yayin da Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a  Gaza

0200 GMT — An ji karar fashewar wasu abubuwa kusa da jirgin ruwa a gabar tekun Yemen a yayin da Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a Gaza

Hukumar kula da tsaron jiragen ruwa ta Birtaniya UKMTO ta ce an samu wata gagarumar fashewa kusa da jirgin ruwan daukar kaya a Zirin Bab al Mandeb, wanda ya raba Yankin Larabawa da Kusurwar Afirka.

Hukumar ta ce ta samu rahotanni na fashewar abubuwa har sau uku daga jirgin ruwan, wanda yake kan hanyarsa da ke tsakanin Eritrea da Yemen.

"Ba a samu rahoton lalacewar jirgin ruwan ba kuma a halin da ake ciki matukansa na cikin koshin lafiya," in ji hukumar kula da tsaron jiragen ruwa ta Birtaniya, wadda ke karkashin Rundunar Sojojin Ruwa ta Birtaniya, a wani takaitaccen sako da ta fitar.

Ta kara da cewa "hukumomi suna gudanar da bincike" kan lamarin.

A makonnin baya bayan nan, 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun kaddamar da jerin hare-hare da jirage marasa matuka da rokoki kan jiragen ruwan kasuwanci da ke wucewa ta Bahar Maliya da Zirin Bab al Mandeb wanda ya hada Bahar Maliya da Gabar Tekun Aden.

Sun ce suna daukar matakan ne domin nuna goyon baya ga Falasdinawa wadanda Isra'ila ke kai wa hare-hare babu kakkautawa a Gaza.

'Yan tawayen na Houthi sun yi gargadi cewa za su kai hari kan jiragen ruwan da ke da alaka da Isra'ila wadanda ke wucewa ta Bahar Maliya.

0158 GMT — Faransa ba za ta goyi bayan kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa a Gaza ba

Faransa ba za ta goyi bayan kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza ba, a cewar Nicolas de Riviere, wakilin kasar na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.

"Faransa tana adawa da korar mutane daga matsugunansu da karfin tsiya. Wannan a bayyane yake...Ba za mu amince da korar mutane daga matsugunansu da karfin tuwo ba," in ji de Riviere a hira da manema labarai.

"A fili yake karara cewa Zirin Gaza wurin zaman Falasdinawa ne. Burinmu shi ne Falasdinawa su samu damar ci gaba da kasancewa cikin lumana da tsaro. Wannan shi ne babban burinmu."

#