Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0715 GMT — An harba rokoki daga Gaza zuwa Tel Aviv
'Yan sandan Isra'ila sun ce an harba rokoki da dama daga Gaza zuwa birnin Tel Aviv da yankunan da ke makwabtaka da shi.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta ambato 'yan sanda suna cewa wani makamin roka ya fada a wan sarari a birnin Rishon Lezion nkusa da Tel Aviv.
Qassam Brigades, wato fannin soji na kungiyar Hamas, ya ce shi ne ya harba rokokin a Tel Aviv domin yin raddi kan kashe fararen-hula da Isra'ila ke yi a Gaza.
0600 GMT — Sarkin Jordan ya ce an wurga 'magunguna na bukatun gaggawa' a Gaza
Jiragen sojin saman Jordan sun wuwwurga magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitocin tafi-da-gidanka da ke yankin Gaza da aka mamaye, a cewar Sarki Abdullah II da safiyar Litinin.
"Sojojin samanmu marasa tsoro sun jefa magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitin wucin-gadi na Jordan da ke Gaza," in ji sarkin a sakon da ya wallafa a shafin X.
0534 GMT — Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta aika da jirgin ruwan nukiliya Gabas ta Tsakiya
Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta ce aika da jirgin ruwan nukiliya yankin Gabas ta Tsakiya.
“Ranar 5 ga watan Nuwamba, jirgin ruwa samfurin Ohio-class ya isa yankin da ke karkashi ikon Amurka,” in ji sanarwar da Cibiyar Tsare-Tsare ta Amurka (CENTCOM) ta wallafa a shafin X.
Amurka ta aika da jirage biyu yankin Gabas ta Tsakiya tun daga ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar da farmakin Operation Al Aqsa Flood a Isra'ila.
0400 GMT — Adadin mutanen da suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 9,770
Ma'aikatar Kiwon Lafiya a Gaza ta ce ya zuwa ranar Lahadi mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Zirin Gaza sun kai 9,770.
“Mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba sun kai 9,770, cikinsu har da kananan yara 4,800 da mata 2,550,” in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
Ta kara da cewa a cikin awa 24 da suka wuce Isra'ila ta kashe Falasdinawa 270.