Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 202. An kashe aƙalla Falasɗinawa 34,262 - galibinsu jarirai da yara da mata. An raunata wasu sama da 77,229. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗay

Kai-tsaye: An fitar da Ben-Gvir daga wajen da Isra'ilawa masu zanga-zanga suka yi wa ƙawanya

0201 GMT — An fitar da Ben-Gvir daga wajen da Isra'ilawa masu zanga-zanga suka yi wa ƙawanya

'Yan sandan Isra'ila sun fitar da minista mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir daga wani gini da ke Yammacin Birnin Ƙudus wanda masu zanga-zanga suka kewaye, ciki har da iyalan wadanda ake garkuwa da su a Gaza.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, daruruwan masu zanga-zangar ne suka taru a yankin da ke kusa da ginin inda ministan kula da kayayyakin tarihi na kasar Amchai Eliyahu na masu tsattsauran ra'ayi da malamin addinin kirista Bentzi Gopstein suka raka Ben-Gvir.

Rundunar ‘yan sandan ta fitar da fitaccen ministan daga wajen da lamarin ya faru bayan jami’anta sun cece shi.

Sun hana masu zanga-zangar isa ga Ben-Gvir ne bayan sun kewaye motarsa ​​suna rera taken rashin amincewa da shi da suka hada da "Shame on you," wato "Ka ji kunya."

'Yan sandan sun yi amfani da hanyoyin tarwatsa jama'a, ciki har da watsa wa mutane ruwan datti, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

#