Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ya shiga kwana na 311, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,790 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum sama da 91,702, yayin da mutane fiye da 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.

Kai-tsaye: Amurka ta tura jiragen yaƙi samfurin F-35 da jiragen ruwa zuwa Gabas ta Tsakiya

Litinin, 12 ga watan Agusta, 2024

0104 GMT — Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya bayar da umarni a tura jirgin ruwa mai ɗauke da makamai masu linzami zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon.

A tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant, Austin ya jaddada aniyar Amurka ta ɗaukar "kowane irin mataki" domin kare Isra'ila, in ji wata sanarwa da Pentagon ta fitar.

"Domin jaddada wannan matsayi, Sakatare Austin ya bayar da umarni a tura jirgin ruwa mai suna USS ABRAHAM LINCOLN, mai ɗauke da jiragen yaƙi samfuran F-35C, domin hanzarta isa cibiyar bayar da umarni, baya ga matakin da aka ɗauka na tura jirgin ruwa na USS THEODORE ROOSEVELT tun da farko," a cewar sanarwar.

Bugu da ƙari, Austin ya bayar da umarni a tura jirgin ruwa na USS Georgia (SSGN 729) mai ɗauke da makamai masu linzami zuwa cibiyar bayar da umarnin soji da ke yankin.

Kazalika jami'an tsaron sun tattauna kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza da kuma muhimmanci rage kashe fararen-hula, da ci gaban da aka samu a tattaunawar tsagaita wuta da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza, da kuma yunƙurin Amurka na "hana" Iran da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da sauran ƙungiyoyi da ke goyon bayan Iran kai hare-hare, a cewa Pentagon.

#