Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0730 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa shida a harin da ta kai Gabar Yamma da Kogin Jordan
An kashe Falasdinawa shida tare da raunata wasu a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a sansanin Tulkarim da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Isra’ila ya tabbatar.
Sojojin na Isra’ila sun kaddamar da samame a sashen kula da marasa lafiya na gaggawa na Asibitin Thabet Thabet da ke Tulkarim.
Haka kuma rahotanni sun ce an kashe wani Bafalasdine a yankin Qalqilya.
0700 GMT — Amurka da Rasha sun yi maraba da yarjejeniyar musayar fursunonin yaki ta Isra’ila da Hamas
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa ya ji dadi matuka kan cewa za a saki wasu daga cikin wadanda Hamas ke rike da su a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa.
Mista Biden din ya bayyana cewa an saki Amurkawa biyu wadanda aka kama a karshen watan Oktoba bayan an yi tattaunawa ta diflomasiyya mai zurfi.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa kasarta na maraba da wannan yarjejeniya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na RIA na kasar ya ruwaito.