Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, wanda yanzu yake kwana na 356, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,495. Bugu da ƙari, sama da mutum 620 aka kashe tun ranar 23 ga watan Satumba a wani babban harin bam da Isra'ila ta kai a Lebanon.

Kai-tsaye: Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai a Gaza ya haura 41,500 - Ma'aikatar Lafiya

Alhamis 26 ga watan Satumban 2024

1235 GMT –– Akalla Falasdinawa 41,534 ne aka kashe tare da jikkata 96,092 a farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma'aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.

0756 GMT — Har yanzu Isra'ila na kai hare-hare yayin da babu tabbas kan tsagaita wuta

Duk da kiran da kasashen duniya suke yi na tsagaita wuta na wucin gadi tsakanin Isra'ila da Hezbollah, sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari a wasu wurare 75 a Lebanon cikin daren Alhamis.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce, jiragen yaƙi sun kai hari kan abin da ta kira rumbun adana makamai na kungiyar Hezbollah, da harba rokoki a kan sauran kayayyakin more rayuwa da gine-ginen soji da 'yan kungiyar ta Lebanon ke amfani da su.

Rundunar ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare ta sama a kasar Lebanon domin lalata abin da ta kira karfin kungiyar Hezbollah.

Hare-haren sun zo ne duk da kiran da Amurka da EU, da wasu ƙasashe tara suka yi a yammacin Laraba ga Isra'ila da Hizbullah da su amince da tsagaita wuta na kwanaki 21 don "ba da sararin diflomasiyya".

0844 GMT — Jirgin sama marar matuƙi na Iraƙi ya afka wa tashar jiragen ruwa ta Eilat ta Isra'ila

Kamfanin tsaro na Birtaniya Ambrey ya ce daya daga cikin jiragen yaki marar matuki guda biyu da mayakan Iraƙi suka harba a jiya Laraba ya kai hari tashar jiragen ruwa ta Eilat ta Isra'ila, inda aka ce ta yi ɓarna tare da jikkata mutane biyu.

0752 GMT — Harin Isra'ila ya kashe 'yan Syria 23 a garin Younine na Lebanon

0752 GMT — Magajin garin Ali Qusas ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akalla mutum 23 dukkansu ‘yan kasar Syria da akasarinsu mata ne ko kuma kananan yara suka mutu a harin da Isra’ila ta kai kan wani bene mai hawa uku a garin Younine na kasar Lebanon da yammacin jiya Laraba.

Qusas ya ce wasu mutum takwas sun samu raunuka.

#