Isra'ila ta kwashe kwana 260 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,431 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 85,653, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500.
0924 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya haura 37,500
Akalla Falasdinawa 37,551 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza tun watan Oktoban bara, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu mutane 85,911 kuma sun jikkata a harin, galibi mata da kananan yara.
"Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 101 tare da jikkata wasu 169 a cikin sa'o'i 24 da suka wuce," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
2253 GMT — Hamas ta ce za ta amince da duk wani tsari da zai kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza
Ismail Haniyeh, shugaban ƙungiyar Hamas da ke gwagwarmayar kare Falasɗinawa, ya jaddada matsayarsu cewa ƙofarsu a buɗe take game da duk wata tattaunawa da za ta kawo ƙarshen kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza idan hakan ya dace da buƙatunsu.
Haniyeh ya bayyana haka ne a wata lacca a birnin Beirut inda aka tattauna game da hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.
Shugaban Hamas ya ce a shirye ƙungiyarsu take ta bayar da haɗin kai game da "duk wata yarjejeniya ko tsari da zai tabbatar da matsayarmu a tattaunawar tsagaita wuta."
Ya jaddada matsayar Hamas ta kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, da janyewar Isra'ila daga yankin da sake gina shi da kai kayan agaji da kuma yin musayar fursunoni.
2030 GMT —Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19, ciki har da waɗanda suka dawo daga aikin Hajji
Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19 a wani samame da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan kafin asubahi, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA, wanda ya ambato majiyoyi da dama.
Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19 a wani samame da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan kafin asubahi, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA, wanda ya ambato majiyoyi da dama.
Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa biyu waɗanda suka dawo daga aikin Hajji a kan iyaka da Jordan, in ji WAFA. An sace sauran mutanen ne a garuruwan Tulkarm, Nablus, Yatma, da Ramallah.
An sace mutanen ne ba tare da wani sammaci ba, kuma dakarun Isra'ila sukan yi irin wannan garkuwa da Falasɗinawa a duk inda Isra'ila ta ga damar yin amfani da ƙarfin-tuwo don cin zarafin Falasɗinawa.
Sojojin Isra'ila sun sace tare da ɗaure Falasɗinawa sama da 9,500 tun daga watan Oktoban da ya gabata, idan aka kwatanta da Isra'ilawa 116 da Hamas da sauran ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa suke tsare da su a Gaza tun wancan lokacin.
1930 GMT — Kashi 76 na makarantun Gaza suna buƙatar a sake gina su: UNRWA
Hukumar kula da Falasɗinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNRWA, ta ce kashi 76 na makarantun Gaza suna buƙatar a sake gina su baki ɗaya.
"A Gaza, fiye da kashi 76 na makarantu suna buƙatar a sake gina su idan ana so a yi amfani da su," a cewar wata sanarwa da ƙungiyar samar da ilimi ta the Global Education Cluster ta ambato UNRWA tana bayyanawa.
UNRWA ta ƙara da cewa duk da yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, tawagarta "tana ci gaba da isa ga ƙananan yara wajen koyar da su da kuma yi musu wasa," tana mai jaddada cewa "ilimi shi ne babban 'yancin da ɗan'adam yake da shi" sannan ta nanata kiran da ta yi na daina kai hare-hare a yankin.