Tsawon kwanaki 102, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,100 da raunata mutum 60,834.
1025 GMT — Adadin Falasdinawan da aka kashe a Gaza ya kai 24,285
Ma’aikatar Lafiya a Gaza da ke Falasdinu ta ce zuwa yanzu akalla mutum 24,285 Isra’ila ta kashe tun daga 7 ga watan Oktoba a Gaza.
Ma’aikatar a wata sanarwa da ta fitar ta ce zuwa yanzu Isra’ilar ta raunata mutum 61,154 a Falasdinu baki daya.
0931 GMT — Isra'ila ta ce ta kai hari iyakar Lebanon domin 'kawar da barazana'
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa sojojinta na musamman sun kai hari yankunan Ayta ash Shab da ke Lebanon.
“Dakarun IDF na musamman sun kai hari domin kawar da barazana daga yankin Ayta ash Shab da ke Lebanon,” kamar yadda sojoji suka bayyana.
Haka kuma sojojin sun ce jirgin yakin su ya kai hari kan wata mota mai harba makami mai linzami a kudancin Lebanon mallakar kungiyar Hezbollah ta Iran.