Sojojin sun ce sun samu nasarar ne sakamakon bayanan sirrin da suka samu kan ‘yan ta’addan.

Jiragen sojin Nijeriya sun yi luguden wuta kan 'yan ta'adda da suka buya a karkashin bishiyoyi a Borno

Rundunar sojin saman Nijeriya ta tabbatar da cewa kusan ‘yan ta’adda 20 ta halaka a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

Lamarin ya faru ne a karshen makon da ya gabata inda rundunar ta ce ta samu gagarumar nasara a kan ‘yan ta’addan.

A wata sanarwa da daraktan watsa labarai na sojin saman kasar Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a ranar Litinin, sojojin sun samu nasarar ne sakamakon bayanan sirrin da suka samu kan ‘yan ta’addan.

“Bayan bayanan sirrin da aka samu daga sojojin kasa na Operation Hadin Kai a ranar 29 ga watan Oktoban 2023, kan cewa an hangi ‘yan ta’adda kusan 22 a cikin motar girke bindiga da babura biyu a kusa da Marte, sai nan take aka tura sojojin sama na OPHK zuwa wurin,” in ji sanarwar.

“Bayan duba wurin, sai aka hangi ‘yan ta’addan kusan kilomita 22 a yammacin Marte inda suke tafiya arewaci ta Munguno. Bayan bin sawun ‘yan ta’addan na kusan mintuna 70, sai ‘yan ta’addan da ke cikin motar girke bindigan da babura biyu suka tsaye karkashin wasu itace, watakila domin su kara mai da kuma guje wa idon mutane,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

Daga nan ne aka bude wuta kan maboyar tasu, inda aka lalata motar girke bindigar da baburan ba tare da wasu alamu na motsi ba.

Rundunar sojin saman ta bayyana cewa idan aka yi la’akari da irin kara fashewar da aka ji, watakila wuri ne na ajiye motarsu ko kuma motar na dauke ababen fashewa masu yawa.

Duk da hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa a arewacin Nijeriya, amma duk da haka sojojin kasar suna ikirarin samun nasara a wasu lokutan.

Domin ko a kwanakin baya sai da sojojin saman kasar suka ce sun kashe ‘yan ta’adda da dama sannan sun lalata babura sama da 40 da motocin girke bindiga shida.

#