A wajen liyafar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Laraba, Tinubu ya ce ba dukkan gangamin yaƙin neman zaɓen shi zai halarta ba, domin kada gangamin ya ɗauke hankalinsa daga hidimar da yake wa ƙasar.

NEWSTIMETR
NEWSTIMETR
Jihohi 12 da Tinubu zai je yaƙin neman zaɓen Nijeriya na 2027

Shugaba Bola Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki ne a jihohi 12 gabanin zaɓukan 2027.

Jadawalin yaƙin neman zaben da jam’iyyar APC ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa ana tsammainin Tinubu ya ƙaddamar da kamfe ɗin sake zaɓensa ne a jihar Kaduna ranar 24 ga watan Oktoba kafin ya halarci gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohi 11.

Bayan gangamin yaƙin neman zaɓen na Kaduna, shugaban zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓe a jihar Ribas da ranar 7 ga watan Nuwamba da Filato 14 ga watan Nuwamba da Oyo a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Ana kuma tsammannin zai halarci kamfe a jihohin Borno da Enugu da Bauchi a ranakun 25 da 28 da kuma 29 ga watan Nuwamba.

Sai dai kuma Tinubu ba zai halarci kamfe na yaƙin neman zaɓe ba a jihohi 13 a cikin watan Nuwamba, kamar yadda jadawalin ya tsara.

Jihohin su ne Cross River (2 ba watan Nuwamba) da Gombe (3 ga watan Nuwamba) da Nasarawa (4 ga watan Nuwamba) da Ekiti (5 ga watan Nuwamba) da Ebonyi (9 ga watan Nuwamba) da Jigawa (10 ga watan Nuwamba) da Ondo (11 ga watan Nuwamba ) da Edo (12 ga watan Nuwamba ) da Yobe (16 ga watan Nuwamba) da Kebbi (17 ga watan Nuwamba) da Akwa Ibom ( 18 ga watan Nuwamba ) da Anambra (19 ga watan Nuwamba) da Benue (30 ga watan Nuwamba).

Ana sa ran Tinubu zai ci gaba da kamfe ɗinsa a watan Disamba da gangamin da aka shirya yi a jihar Sokoto ranar 5 ga watan Disamba da jihar Delta a ranar 12 ga watan Disamba da kuma jihar Kano a ranar 17 ga watan Disamba.

Zai ƙarƙare fita yaƙin neman zaɓen ne a jihar Adamawa ranar 4 ga watan Janairu da kuma jihar Legas ranar 9 ga watan Janairu, yayin da shuwagabannin jam’iyyar za su wakilce shi a gangamin yaƙin neman zaɓe a sauran jihohi 12 a watan Disamba.

Jumulla dai ana tsammain Tinubu zai halarci yaƙin neman zaɓe ne a 12 daga cikin jihohin Nijeriya 36 da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Huɗu daga cikin jihohin da ake sa ran Tinubu zai ziyarta — Kano da Oyo da Bauchi da Adamawa — suna da jigajigan ‘yansiyasar jam’iyyun hamayya da ke alaƙa da takarar shugaban ƙasa na 2027.

Tsohon gwmanan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ɗantakaran mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC kuma ɗan jihar Kano ne.

Shi kuwa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya kuma ɗantakaran shugaban ƙasa a jami’yyar ADC, Atiku Abubakar, ɗan jihar Adamawa ne.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, shi ne ɗantakaran shugaban ƙasa a jam’iyyar APM, wadda ita ce jam’iyya mai mulki a jihar Bauchi.

A wajen liyafar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Laraba, Tinubu ya ce ba dukkan gangamin yaƙin neman zaɓen shi zai halarta ba, domin kada gangamin ya ɗauke hankalinsa daga hidimar da yake wa ƙasar.

Sai dai kuma ya ce shi zai ware lokacin da zai yi amfani da shi wajen magana kai-tsaye da ‘yan Nijeriya yayin da shuwagabannin jam’iyyar ke yawo a faɗin jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar wajen yaƙin neman sake zaɓarsa.

A ranar Talata ne dai APC ta ce ta faɗaɗa jerin sunayen ‘yankwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar inda ta ƙara sunayen minsitan Abuja Nyesom Wike da gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke da gwmanan jihar Anambara Chukwuma Soludo a cikin wasu manyan ƙusoshi da ta ƙara.

#