Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Sai dai biyu daga sojojin Nijeriya da kuma wani ɗan bijilante ɗaya sun rasa ransu yayin fafatawar, kamar yadda sanarwar ta sojin Nijeriya ta bayyana.

Jami'an tsaron Nijeriya sun hallaka 'yan bindiga 19 a Jihar Kano

Rundunar sojan Nijeriya ta ce jami’anta da sauran jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 19 a karamar hukumar Shanono da ke jihar Kano, tare da ƙwato babura da dama a wata musayar wuta da aka yi tsakanin bagarorin biyu.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar, bayan samun wasu bayanan sirrin da suka nuna cewa ‘yan bindigar suna kai-kawo a wasu yankuna na ƙaramar hukumar ta Shanono.

Sai dai biyu daga sojojin Nijeriya da kuma wani ɗan bijilante ɗaya sun rasa ransu yayin fafatawar, kamar yadda sanarwar ta sojin Nijeriya ta bayyana.

Sanarwar, wacce Babatunde Zubairu mataimakin jami’in hulda da jama’a na Runduna ta Uku ta sojan Nijeria da ke Kano ya fitar, ta ce an samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar daga Shanono a yayin gagarumar arangamar da aka yi.

Ta kara da cewa, “a yanzu haka ana ci gaba da gudanar da aikin tsaro a yankin, don bai wa jama’a kariya, waɗanda ‘yan fashin dashi ke yawan addabar su da satar shanu.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#