Sport
Dollar
42,3350
0.2 %Euro
49,1712
0.05 %Gram Gold
5.547,4900
-0.07 %Quarter Gold
9.430,0100
0 %Silver
69,2000
0.51 %Rahotanni sun ce an samu yamutsi a hedikwatar jam'iyyar a babban birnin Nijeriya Abuja, kafin Turaki ya yi jawabi ga manema labarai.
Kabiru Turaki, Shugaban jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya ya ce jam’iyyar ta ɗaga zaman farko na kwamitin gudawarwarta wanda ta shirya yi ranar talata a Abuja.
Da yake magana da manema labarai bayan ya samu shiga cikin hedikwatar jam’iyyar a ginin Wadata Plaza, Turaki ya ce an ɗauki wannan matakin ne sakamakon “ayyukan masu yi wa Dimokuraɗiyya karan-tsaye”.
Ya ce yanzu za a yi zaman ne ranar Laraba 19 ga watan Nuwamba.
Turaki, wanda yake tare da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya yaba wa kwamishinan ‘yan sandan Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, saboda irin tsaron da ya bai wa shugabannin jam’iyyar, har suka samu damar shiga hedikwatarta.
Ya ce shi ya yi wa kwamishinan bayani game da shirin kwamitin gudanawar jam’iyyar da aka shirya yi da kuma “takardun da suke yawo a shafukan sada zumunta” da ke shelar zaman kwamitin zartarwa da kwamitin amitattu na wasu mutane da tuni suka bar jam’iyyar.
Ya ce ‘yan sanda sun cika alƙawarinsu wajen tabbatar da cewa shugabannin jam’iiyar sun iya shiga harabar domin yi wa manema labarai jawabi.
Turaki ya gode wa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayanusu, yana mai cewa jam’iyyar PDP ta amice wajen tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya.
Ya ce gwamnonin da ‘yan majalisar dokokin ƙasa da tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci da kuma waɗanda suka bar kwamitin amittatun jam’iyyar kwanan nan sun nuna haɗin kai, inda suka raka shi hedikwatar jam’iyyar.
Ya ce PDP ta mayar da hankalinta kan dawo da ƙarfinta, kuma dole ta fara tabbatar da haɗin kai a faɗin ƙasar kafin ta iya komawa mulki.
Ɗage zaman na zuwa ne yayin da ake rikicin shugabancin da ya raba jam’iyyar gida biyu, inda ɓangaren Turaki ke jaddada dacewarsa bayan ya kori Samuel Anyanwu, tsohon sakataren jam’iyar.
Comments
No comments Yet
Comment