Kocin Galatasaray, Okan Buruk, na fatan samun nasararsa ta 150 a matsayin kocin ƙungiyar a wasan da za su yi da Barcelona.

Istanbul ta cika da ɗoki da karsashi gabanin wasan Galatasaray da Barcelona a Gasar Zakarun Turai

An shiga yanayin ɗoki da farin ciki a Istanbul gabanin wasan da Galatasaray za ta karɓi baƙuncin Barcelona a Gasar Zakarun Turai ta Champions League a ranar Talata, da ƙarfe 10 na dare agogon Turkiyya (7 na yamma agogon GMT).

Ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya na neman farfaɗowa daga rashin nasara da ci 3-1 da ta yi a hannun Sporting a wasanta na farko na gasar, yayin da Barcelona ke zuwa wasan bayan ta doke Feyenoord da ci 5-1.

Galatasaray za ta buga wasan ba tare da mai tsaron bayanta da ya ji rauni, Wilfried Singo ba. Shi ma ɗan wasan gaba na Barcelona, Raphinha, ba ya cikin tawagar da za ta buga wasan. Alƙalin wasa Marco Guida daga Italiya ne zai jagoranci fafatawar.

Kocin Galatasaray, Okan Buruk, na fatan samun nasararsa ta 150 a matsayin kocin ƙungiyar a wasan da za su yi da Barcelona.

Buruk, wanda ya karɓi ragamar horar da ƙungiyar gabanin kakar wasa ta 2022–2023, ya samu nasarori 149, kunnen doki 29 da rashin nasara 33 a wasanni 211 da ya jagoranta a dukkan gasa.

Zazzafar muhawara da nuna ɗoki sun bazu har zuwa shafukan sada zumunta. A ranar 12 ga Oktoba, shafin Barcelona na hukuma ya wallafa saƙon, “Sannu, Istanbul, mun iso,” lamarin da ya jawo martani da dama daga magoya bayan Galatasaray a shafin X.

Wasu sun rubuta cewa, “Muna jiranku,” yayin da wasu suka ce, “Za ku koma yadda kuka zo.” Wasu kuma sun wallafa barkwanci da bidiyoyin maraba da tawagar ta Sifaniya zuwa Istanbul.

Ita ma Galatasaray ta fitar da wani ɗan gajeren bidiyon tallata wasan, wanda ya ƙara ɗaga hankalin magoya bayanta yayin da suke shirin tarbar ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai.

Galatasaray ta yi nasara a wasanni huɗu cikin shida na baya-bayan nan da ta buga a gida a Champions League. Haka kuma, tana da damar samun nasara a wasannin gida uku a jere a gasar a karon farko tun shekarar 2001.

A nata ɓangaren, Barcelona ta zura ƙwallaye 80 a wasanni 27 na Champions League ƙarƙashin jagorancin kocinta, Hansi Flick, a cewar bayanin wasan da Galatasaray ta wallafa.

Zakarun Turkiyya za su yi ƙoƙarin amfani da goyon bayan dubban magoya bayansu a filin wasa na RAMS Park wajen samun sakamako mai kyau a kan Barcelona, yayin da kowace ƙungiya ke neman ƙarfafa matsayinta a matakin rukuni na gasar.

A karo na ƙarshe da ƙungiyoyin biyu suka fafata da juna, a watan Maris na shekarar 2022, Barcelona ce ta yi nasara da ci 2-1 a filin wasa na RAMS Park na Istanbul.

#