Tsawon kwanaki 102, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,100 da raunata mutum 60,834.
1631 GMT — 'Yan Houthi sun kai hari kan jirgin ruwan Zografia mai zuwa Isra'ila — jami'ai
Kakakin rundunar Houthi Yahya Sarea ya ce mayakan ƙungiyar ta Yaman sun kai hari kan jirgin ruwan Zografia da ke kan hanyarsa zuwa Isra'ila da makamai masu linzami na ruwa wanda ya yi sanadin samun jirgin kai tsaye.
Wasu majiyoyin ma'aikatar sufurin jiragen ruwa na kasar Girka guda biyu sun ce, jirgin mai dauke da tutar Malta, mallakin kasar Girka, ya lalace, amma babu wanda ya ji rauni, bayan da aka same shi a cikin Bahar Maliya kusa da tashar jiragen ruwa ta Saleef na kasar Yemen.
1308 GMT — Israila ta ƙaddamar da jerin hare-hare a kudancin Labanon
Sojojin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare ta sama da kuma luguden wuta a birnin Wadi Saluki na kudancin kasar Lebanon, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka bayyana.
Kamfanin dillancin labaran Isra'ila na KAN ya rawaito cewa jiragen yakin Isra'ila sun kai farmaki kan wasu wurare da dama na kungiyar Hizbullah a yankin, da suka hada da wuraren leƙen asiri da gine-ginen soji, da sauran ababen more rayuwa na kungiyar Hizbullah.
Kamfanin dillancin labaran kasar Labanon ya ce Isra'ila ta kai hare-haren ne kan Wadi Saluki da Houla da Wadi al Hujeir da Rab El Thalathine da Kfarkela da Meiss al-Jabal.
A nata bangaren, kungiyar Hizbullah ta ce mayakanta sun kai hari da makami mai linzami a wurin taron sojojin Isra'ila a gabashin matsugunin Even Menahem a arewacin Isra'ila.
1209 GMT — Hare-haren da ake kai wa Tekun Maliya na da alaƙa da yakin Gaza, akwai buƙatar tsagaita wuta — Ministan Harkokin Wajen Saudiyya
Saudi Ministan Harkokin Wajen Saudiyya ya ce hare-haren da 'yan Houthi ke kai wa kan jiragen ruwa na kasuwanci a Tekun Maliya na da alaƙa da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, kuma akwai buƙatar a tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba.
A yayin Taron Tattalin Arziki na Duniya (WEF) da ake yi a Davos, Yarima Faisal bin Farhan Al Saud ya ce babban abin da ƙsarsa ta fi bai wa fifiko shi ne gano wata hanya ta yayyafa wa lamarin ruwa ta hanyar tsagaita wuta a Gaza.
1016 GMT — 'Makaman roka da aka harba Isra'ila daga Gaza na daga cikin mafiya ƙarfi'
Isra'ila ta ce an harba makaman rokoki 15 zuwa kudancin Isra'ila, inda suka lalata wani shago.
Kafar yaɗa labaran Isra'ila ta ce lamarin na daga cikin hare-hare mafi ƙarfi da aka kai daga Gaza a cikin fiye da mako ɗaya.
Gidan talabijin na Channel 12 ya rawaito cewa an ƙaddamar da harba rokokin ne daga garin Bureij da ke tsakiyar Gaza.
Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da Ministan Tsaro Yoav Gallant ya ce rundunar sojin Isra'ila na faɗaɗa ƙrfin ikon sojinta a arewacin Gaza zuwa sauran yankunan da ke zirin.
1025 GMT — Adadin Falasdinawan da aka kashe a Gaza ya kai 24,285
Ma’aikatar Lafiya a Gaza da ke Falasdinu ta ce zuwa yanzu akalla mutum 24,285 Isra’ila ta kashe tun daga 7 ga watan Oktoba a Gaza.
Ma’aikatar a wata sanarwa da ta fitar ta ce zuwa yanzu Isra’ilar ta raunata mutum 61,154 a Falasdinu baki daya.
0931 GMT — Isra'ila ta ce ta kai hari iyakar Lebanon domin 'kawar da barazana'
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa sojojinta na musamman sun kai hari yankunan Ayta ash Shab da ke Lebanon.
“Dakarun IDF na musamman sun kai hari domin kawar da barazana daga yankin Ayta ash Shab da ke Lebanon,” kamar yadda sojoji suka bayyana.
Haka kuma sojojin sun ce jirgin yakin su ya kai hari kan wata mota mai harba makami mai linzami a kudancin Lebanon mallakar kungiyar Hezbollah ta Iran.