Tsawon kwanaki 132, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,576 da raunata mutum 68,291.
1442 GMT — Isra'ila tana aikata kisan kiyashi ba tare da wata shakka ba - Jami'in MDD
Mutum sama da miliyan ɗaya da suka yi gudun hijira daga Gaza zuwa birnin Rafah da ke kudancin yankin, na cikin fama da matsanancin ƙaranci abinci da ruwa da tsaftar muhalli, da sauran buƙatu na yau da kullum, kamar yadda wani wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman ya shaida wa Anadolu.
"Sama da mutum miliyan daya ne suke cunkushe a Rafah, wadanda suka yi gudun hijira daga wasu sassan Gaza, kuma suna fama da ƙarancin kayan masarufi na yau da kullum, daga abinci da ruwa da tsaftar muhalli tare da barazanar cututtuka fiye da duk wani abu da muka gani na wani rikici a cikin 'yan shekarun nan a duniya," in ji Balakrishnan Rajagopal, wakilin MDD na musamman kan 'yancin samun gidaje.
Ya ƙara da cewa "Ba a taɓa samun wani yanayi da ba za ma a bar jama'a ko guduwa su yi ba."
Yayin da yake jaddada yadda masu aiko da rahotanni na MDD suka rubuta rahotanni da dama kan "kisan kare dangi" na hare-haren Isra'ila a Gaza, Rajagopal ya bayyana cewa, sun ambaci "mummunan hadarin kisan kiyashi" a cikin rahotonsu na farko.
1225 GMT — Yunkurin samar da zaman lafiya a Gaza ba ya tasiri saboda tsarin Amurka - Erdogan
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce kiraye-kirayen zaman lafiya a Gaza, inda Isra'ila ta kashe sama da mutum 28,000, "abin takaici ne yadda ya kasance ba ya wani tasiri saboda mummunan tsarin Amurka."
"Duk da cewa Amurka ta yi ikirarin tura wasu manyan jami'ai zuwa yankin don samo mafita, bisa ga dukkan alamu ba a cimma wani sakamako na gaske ba. Duk da halin da ake ciki, muna ci gaba da kokarin ganin an tsagaita wuta da samar da zaman lafiya, saboda ba mu ga wata mafita ta daban ba," in ji Erdogan.
"Dole ne ɗan'adam ya ji wannan koken da wuri-wuri. Ci gaba da yin shiru kan wannan kisan ƙare dangi nauyi ne babba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "Tarihi zai hukunta wadanda suka ba da izinin kashe wadannan mutane da gangan, wadanda ke da hannu a wannan kisan kiyashin sun riga sun shiga tarihi a matsayin masu laifi."
1001 GMT — Dakarun Isra'ila sun kutsa cikin Asibitin Nasser Hospital na Khan Younis
Dakarun Isra'ila sun kutsa cikin babban asibitin da ke kudancin Gaza awanni kadan bayan sojojin ƙasar sun kashe wani majinyaci sannan suka jikkata marasa lafiya shida a harabarsa, in ji ganau.
Kakakin Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu Ashraf al Qidra ya ce Isra'ila ta ƙaddamar da "gagarumin kutse" tare da harbe-harbe da suka raunata mutanen da dama da suka samu mafaka a asibitin bayan sun rasa matsugunansu.
Ya ce sojojin sun umarci likitoci su kwashe dukkan marasa lafiya daga tsohon ginin asibitin wanda ba a sanya masa kayayyakin aikin da suka kamata ba na kula da masu jinya.
0409 GMT — Ƙasashen Larabawa sun nemi MDD ta dakatar da Isra'ila daga mamaye Rafah
Ƙasashen Larabawa 22 a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar ya nemi a tsagaita wuta nan-take a Gaza da kuma bari a kai kayan agaji da ma hana fitar da kowane Bafalasɗine daga yankin.
Jakadan Tunisia a Majalisar Tarek Ladeb ya bayyana "bala'in da ke fuskantar" Falasɗinawa miliyan 1.5 da ke yankin Rafah na Gaza muddin Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya aiwatar da shirinsa na mamaye yankin.
Mako biyu da suka wuce Algeria ta raba wani daftarin doka wanda yake adawa da tursasa wa mutane barin yankinsu tare da neman a gaggauta tsagaita wuta a Gaza.
Jakadiyar Amurka Linda Thomas-Greenfield ta bayyana damuwarta game da yiwuwar rugujewar tattaunawar tsagaita wuta.
0234 GMT — Isra'ila ta kashe mutum daya a hare-haren da ta kai Asibitin Nasser a Gaza da raunata mutane
Akalla mutum daya ne ya mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da sojojin Isra'ila suka kai a asibitin Nasser da ke kudancin Gaza na Khan Younis, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinu ya rawaito.
An kai harin ne a sashen kula da masu jinyar ƙashi na asibitin, in ji WAFA.
Rahoton ya yi nuni da cewa, a cikin kwanaki 25 da suka gabata ne sojojin Isra'ila suka killace asibitin.
Tun da farko dai sojojin Isra'ila sun tilasta wa dubban Falasdinawa da ke neman mafaka a Asibitin Nasser ficewa.
Shaidun gani da ido sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, sojojin Isra'ila sun umarci mutanen da suka rasa matsugunansu da su fice daga asibitin a karkashin wutar da sojojinta suka yi.
Sun umarce su da su fita cikin jerin gwano su nufi yankunan gabashin Khan Younis.
Wasu shaidun gani da ido sun ƙara da cewa, motocin sojoji na ci gaba da yi wa asibitin ƙawanya, yayin da jami'an tsaron farin kaya ke lalata katangarsa a shirye-shiryen afkawa asibitin.
A ranar Talata Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa da dama a lokacin da suke kokarin fita daga Asibitin Nasser.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce, sun damu matuka game da halin da ake ciki a Asibitin Nasser da ke yankin Zirin Gaza da ke kusa da shi, wanda dakarun Isra'ila suka yi wa ƙawanya.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce "Muna matukar damuwa game da lafiyar marasa lafiya da ma'aikatan kiwon lafiya saboda karuwar tashin hankali a kusa da asibitin.
"Muna maimaita cewa: Dole ne a kare lafiya a kowane lokaci," in ji Tedros Adhanom Ghebreyesus a shafinsa na X, yana sake nanata kiran da ya yi na a samar da zaman lafiya da tsagaita wuta.