'Yan sandan Isra'ila sun bayar da umarni ga dukkan 'yan jarida su fita daga gidan Jaabis gabanin isar ta domin kada su bayar da labari kan halin da take ciki a lokacin da aka sake ta daga kurkuku.

Isra'ila ta saki fitacciyar Bafalasdiniya Israa Jaabis amma ta hana a yi murna

Fitacciyar Bafalasdiniyar nan Israa Jaabis ta isa gidanta a Gabashin Birnin Kudus da aka mamaye bayan sakin ta daga gidan yarin Isra'ila, kamar yadda Cibiyar Wadi Hilweh da ke da hedkwata a Birnin Kudus ta bayyana a ranar Lahadi.

Ta kara da cewa kafin sakin ta, 'yan sandan Isra'ila sun dauki matakai da suka hada da hana gudanar da bikin sakin ta da kuma korar dukkan 'yan jarida da suka isa gidanta domin daukar labarin isar ta.

Jaabis ta kwashe shekara bakwai a kurkukun Isra'ila bayan an yanke mata hukuncin daurin shekara 11.

Ranar 11 ga watan Oktoba na 2015, Jaabis, mai shekara 31, tana kan hanyarta zuwa gida a Birnin Kudus yayin da wata tukunyar gas ta tashi da wuta a cikin motarta. Ta samu munanan raunuka bayan kusan kashi 60 na jikinta ya kone, ciki har da da fuska da hannayenta.

Hukumomin Isra'ila sun zargi Jaabis da yunkurin kaddamar da harin "ta'addanci", zargin da ta musanta.

Jaabis tana cikin rukuni na biyu na Falasdiniyawa 39 mata da kananan yara da Isra'ila ta saka a yarjejeniyar musayar fursunoni da ta kulla da kungiyar da ke fafutukar kare hakkin Falasdinawa ta Hamas.

Dangin Israa Jaabis ne suka tarbe ta a gidanta da ke Birnin Kudus./Hoto: Reuters

An kusa kammala sakar rukuni na biyu na fursunoni

Hamas ta saki 'yan Isra'ila da 'yan wasu kasashen guda 24 yayin da Isra'ila ta saki Falasdinawa 39 da ke gidajen yarinta ranar Juma'a, a yarjejeniyar tsagaita wata ta kwana hudu da suka kulla.

An kusa kammala sakar rukuni na biyu na fursunoni bayan an saki 'yan Isra'ila da 'yan kasashen waje 17 ranar Asabar.

Yarjejeniyar ta bukaci a saki mutanen a matakin rukuni-rukuni cikin kwana hudu.

#