Tsawon kwanaki 129, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,340 da raunata mutum 67,984.
1110 GMT — Isra'ila ta ce an kashe mata sojoji na musamman biyu a kudancin Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojojinta na musamman biyu da raunata uku a yayin wani gumurzu da Falasɗinawa a kudancin Gaza.
Zuwa yanzu adadin sojojin Isra’ila da aka kashe tun bayan fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba ya ƙaru zuwa 566.
Isra’ila ta kashe Falasɗinawa sama da 28,340 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, inda akasarin waɗanda aka kashe yara ne da mata.
1053 GMT — Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah
Sama da mutum 100 Isra'ila ta kashe a hare-haren da ta kai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito.
Birnin na Rafah na daidai iyakar ta Gaza da Masar, wanda wuri ne wanda sojojin Isra'ila suka tilasta wa farar hula gudun hijira inda suke inda suka yi iƙirarin cewa wuri ne mai aminci.
Sojojin Isra'ila a ranar Lahadi sun amince da a kai hari ta ƙasa a Rafah.
Falasdinawa sun nemi mafaka a Rafah a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a sassan Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.