Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 85 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 21,507 tare da jikkata 55,915 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira.
1354 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 100 da raunata 158 a Gaza
Akalla Falasdinawa 100 aka kashe tare da raunata 158 a hare-haren da Isra’il ta kai tsakiyar Gaza a sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda wani babban jami’in lafiya ya bayyana.
Mazauna sansanin ‘yan gudun hijira na biranen Nuseirat da Bureij sun bayar da rahoton cewa Isra’ilar ta shafe dare tana kai musu hari, wadanda sun kasance wurare biyu wadanda Isra’ilar ta fi zafafa hare-hare.
Sakamakon yadda Isra’ilar ke ci gaba da kai hare-hare a cikin Khan Younis da kuma tsakiyar Gaza, dubban Falasdinawa na ci gaba da kwarara birnin Rafah wanda tuni dama ya cika makil da jama’a.
0109 GMT — Isra'ila ta kashe 'yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami'ai
Jami'ai sun ce sojojin Isra'ila sun kashe wani dan jarida a Gaza, abin da ke nufin kawo yanzu sun kashe 'yan jarida 106 tun da suka kaddamar da hare-hare a yankin.
An kashe dan jaridar da ke aiki da gidan talbijin na Al Quds TV tare da wasu iyalansa a hari ta sama da sojojin Isra'ila suka kai gidansu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, a cewar jami'an lafiya da abokansa 'yan jarida.
Kungiyar da ke kare hakkin 'yan jarida ta Committee to Protect Journalists (CPJ) a makon jiya ta ce makonni 10 na farkon yakin da Isra'ila ke yi a Gaza su ne mafi muni da 'yan jarida suka fuskanta, inda wannan shekarar ta kasance wacce aka fi kashe 'yan jarida a wuri daya.
Galibin 'yan jaridar da Isra'ila ta kashe Falasdinawa ne. Rahoton kungiyar CPJ da ke da cibiya a Amurka ya ce ta yi "matukar damuwa musamman kan yadda sojojin Isra'ila suke kai hari kan 'yan jarida da iyalansu da gangan."
A farkon watan nan, wani binciken kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gano cewa wata tankar yakin Isra'ila ce ta kashe dan jaridar Reuters, Issam Abdallah, da kuma jikkata 'yan jarida shida a Lebanon ranar 13 ga watan Oktoba ta hanyar yin luguden wuta a kansu a yayin da suke daukar labarai kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa a kan iyaka.
2343 GMT — An yi tsayuwar dare a London kan 'Kisan Kare-Dangi na 2023' a Gaza
Ma'aikatan kiwon lafiya da 'yan jarida sun yi tsayuwar dare a kofar gidan firaiministan Birtaniya da ke 10 Downing Street domin nuna alhini ga abokan aikinsu da Isra'ila ta kashe a Gaza sannan suka yi kira da a gaggauta tsagaita wuta.
Wadanda suka yi tsayuwar daren, ciki har da fitattun likitoci irinsu su Omar Adel-Mannan, likitan kwakwalwa da Lemis Andoni, fitaccen dan jarida Bafalasdine, sun yi kira a tsagaita wuta nan-take.
Adel-Mannan, wanda a baya ya yi aiki a Gaza, ya gabatar da jawabi mai tsara jiki "mutanen da ba sa magana wadanda su suka fi yawa," inda ya nemi su "fito karara su nemi a dauki mataki kan bala'in da ke faruwa a Gaza."
"Wannan yaki babban bala'i ne. Wannan kisan kiyashi ne. Wannan kare-dangi ne na 2023 domin kuwa wannan shi ne gaskiyar abin da ke faruwa," in ji shi, inda ya fito da irin barnar da ake aikatawa a Gaza.