Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
1610 GMT — Mukaddashin Kakakin Majalisar Dokokin Falasdiniwa ya rasu a harin Isra'ila
Kungiyar Hamas ta Falasdinawa a ranar Asabar ta ce Isra’ila ta kashe Mukaddashin Kakakin Majalisar Dokokin Falasdiniwa a Gaza a yayin wani hari da Isra’ilar ta kai.
“Muna alhinin rasuwar shahidi Ahmed Bahr, mukaddashin Kakakin Majalisar Dokokin Falasdinu wanda ya rasu sakamakon raunukan da ya samu bayan harin bam din da Yahudawa suka kai kan ginin majalisar a yankin zirin Gaza,” in ji sanarwar.
1525 GMT — Wasu kasashen Turai sun haramta gangamin goyon bayan Falasdinawa
Wasu daga cikin Turawan da ke son daga muryarsu domin nuna goyon baya ga Falasdinawa na fuskantar kalubale a kasashen da suke sakamakon haramcin da aka saka kan goyon bayan Falasdinawa da daga tutocinsu.
Tuni Birtaniya da Faransa da Switzerland da Jamus da Jamhuriyar Czech da Austria suka saka irin wannan takunkumin mai tsauri kan jama’ar da ke son fitowa fili don yin Allah wadai da kisan da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza.
Kungiyoyi masu zaman kansu da dama daga ciki har da Amnesty International duk sun caccaki irin dabi’ar da kasashen suka nuna duk da ‘yancin tofa albarkacin baki da ke da akwai a kasashen.
1340 GMT — Isra'ila ta kashe gomman mutane a makarantar Al Fakhoura ta Gaza
Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu a wani hari da Isra’ila ta kai makarantar Al Fakhoura wadda ke dauke da dubban ‘yan gudun hijira a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasdinawa ta ruwaito.
Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu a wata sanarwa da ta fitar ta ce wannan ‘kisan kiyashin’ alama ce da ke nuna cewa yakin Isra’ila na son yi wa arewacin Gaza karkaf.
1300 GMT — Dakarun Al Quds Brigades sun yi ikitarin lalata tankokin yakin Isra'ila
Dakarun Al Quds Brigades na Falasdinawa sun ce sun lalata tankokin yakin Isra’ila biyu da kuma buldoza daya a Gaza, inda suka ce suna ci gaba da kai hari kan sauran kayayyakin soji na Isra’ila.
A wata sanarwa da Al Quds Brigades din ta fitar, ta bayyana cewa ta tayar da bam kan taron makiyanta a cikin dajin Kissufim da ke Zirin Gaza.
Haka kuma kungiyar ta ce dakarun nata sun kai hari kan motocin soji guda bakwai a Tal al Hawa da al Sabra da ke kudu maso yammacin birnin na Gaza.
1230 GMT — Gomman gawawwaki sun isa asibitocin Indonesia da Kamal Adwan da ke Gaza
Gomman gawawwaki sun isa asibitocin Indonesia da Kamal Adwan da ke Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare.
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu da ke Gaza ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.
“Wasu karin gawawwaki shida sun sake isowa Asibitin Al Aqsa sakamakon harin da masu mamaya suka kai gidan Aqtifan da ke Deir Al Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.
0850 GMT — Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki
Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta ce ta kakkabo jirgin Isra’ila maras matuki da makami mai linzami a yankin Galilee Panhandle.
Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar da safe inda ta ce ta harba makamin nata da misalin karfe 1:45 agogon kasar, (23:45 agogon GMT).
Ta bayyana cewa ta hango lokacin da tarwatsatsun sassan jirgin ke fadawa a yankin Galilee Panhandle.
Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da sanarwa domin gasgatawa ko kuma karyata ikirarin na Hezbollah ba.
Sama da Falasdinawa 12,000 Isra’ila ta kashe zuwa yanzu, inda sama da 8,300 yara ne da mata, haka kuma ta raunata sama da 30,000.