"Cibiyar yaki da labaran karya ta Turkiyya ta fitar da wasu karairayi sama da 100 da Isra'ila ke yadawa," a cewar Shugaba Erdogan a yayin jawabinsa a taron koli na dabarun Sadarwa.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba ake ta kai munanar hare-hare tare da kisan kiyashi a zirin Gaza, inda ''aka take duk wani yanci da daraja ta dan Adam'', a cewar Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
'' Isra'ila ta yi ta kokarin hana mutanen da take zalunta damar samun hanyar da za a iya kawo musu dauki wajen katse hanyoyin sadarwarsu da duniya'' in ji Erdogan a yayin jawabinsa a taron kolin dabarun sadarwa na STRATCOM a birnin Istanbul a ranar Juma'a.
''Musammam Isra'ila take kashe 'yan jarida, wadanda duk da irin wahalhalun da ake fuskanta suke kokarin ba da rahoton yanayin bala'in da al'ummar Gaza ke ciki ga duniya,''
Erdoga ya kara da cewa ''ya zuwa yanzu an kashe 'yan jarida sama da 60 a sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa."
Shugaban ya kuma ja hankali kan yadda Cibiyar Yaki da Yada Labarai ta Turkiyya ta bayyana karairayi sama da 100 da Isra'ila ke yadawa tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Shugaban na Turkiyya ya sake jaddada gazawar kungiyoyin kasashen ketare da tsare-tsaren kasashen duniya wajen tunkarar kawo karshen zafafan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.
"Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ya kasance mara amfani a tsarin da aka kafa shi don ya yi aiki sakamakon gaza tabuka wani aikin a zo a gani a halin kuncin da ake ciki a Gaza,'' in ji shi.
Shugaban ya nanata cewa Isra'ila "tana aikata laifin yaki a fili" ta hanyar katse wutar lantarki da ruwa da man fetur da abincin mutanen Gaza.
Rikici a tsarin mulkin kasa da kasa'
Irin hare-haren da Isra'ila ke kaiwa yankin Gaza na Falasdinu ba kakkautawa ya tabbatar da rikicin da ake samu a tsarin mulkin kasa da kasa, a cewar daraktan sadarwar Turkiyya Fahrettin Altun, yayin da yake gabatar da jawabi a taron STRATCOM a Istanbul.
"A tsarin bai daya na duniya, matakan da aka samar a fagen mulkin duniya na ci gaba da rasa tasirinsu." in ji Altun.
Yana mai jaddada cewa, a kasar Siriya, kasashen duniya sun shaida yadda manyan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka nuna gazawarsu ta fuskantar kai taimako a yakin basasa da kuma bala'o'in da aka shiga na jinkai, yayin da yakin Rasha da Ukraine ya nuna rashin karfin tsarin kasa da kasa a rikice-rikice tsakanin kasashe.
Ko da yake irin hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa kawanya, "ba tare da wani dalili ko jinkai ba," ya fito da rikicin da ke cikin tsarin mulkin kasa da kasa wa duniya, in ji Altun.
Labaran karairayi game da Gaza 'sun bayyana a fili'
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan shi ma ya yi jawabi ga mahalarta taron, inda ya bayyana irin halin da duniya ke ciki, wajen bayyana yadda wasu kasashe ke zama masu taimaka wa tsarin da ke ci gaba da tada kayar baya.
Ya ja hankali kan al'amuran da suka faru a baya, kamar shiga tsakani a Afganistan, da kuma rawar da yada bayanan karya suka taka daga hukumomi, sannan ya koka kan sake fadawa irin hakan a rikicin Gaza.
Yayin da a yanzu aka ga yadda yada labaran karya suka fito karara a bayanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza, "akwai bukatar kara inganta dabarun hanyoyin sadarwa na zamani don yaki da bayanar karya," in ji Fidan, yana mai jaddada burin Turkiyya na fahimtar da duniya tun daga tushe da kuma bayyana gaskiya yadda take.
Turkiyya 'na tsaye ita kadai' wajen yaki da ta'addanci
A jawabin nasa, Fidan ya bayyana cikakken tsarin da Turkiyya ke bi wajen tabbatar da tsaro da yaki da ayyukan ta'addanci, inda ya jaddada bukatar hadin kan kasa da kasa domin tunkarar dabarun kungiyoyin 'yan ta'adda.
"Kokarin da muka yi ya sa aka yanke shawarar sabunta takardun yaki da ta'addanci na NATO. Musamman aka nada jami'in da zai na kula ayyukan yaki da ta'addanci, wanda wannan shi ne karon farko da aka fitar da irin wannan matsayi." in ji shi.
Ministan ya kara da cewa, a wasu lokuta, Turkiyya na tsayuwa ita kadai ne a kokarin da take yi na yaki da kungiyoyin ta'addanci irinsu Daesh da PKK wacce ta fadada zuwa kungiyar YPG.
Ya bayyana damuwarsa game da goyon bayan da kungiyar YPG ke samu daga kasashe da ke kawance da ita kamar Amurka, inda ya bayyana hakan a matsayin "kuskure dabaru" tare da jaddada mahimmancin bayyana gaskiya da amince wajen magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a duniya baki daya.