Hukumar ta ce ta kama mutum 5,532 wadanda take zargi da safarar miyagun kwayoyi da tu’ammali da su kuma mutum 210 a cikin mutanen mata ne sai kuma 454 ‘yan kasashen waje ne.
Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi na Nijar OCRTIS ta ce a 2022 jami’anta sun kama miyagun kwayoyi da kudadensu suka kai biliyan 26.
A sanarwar da kakakin hukumar 'yan sanda ta Nijar, Kwamishina Habou Mountari ya fitar, hukumar ta OCRTIS ta kama mutum 5,532 wadanda take zargi da safarar miyagun kwayoyi da tu’ammali da su.
A cewar sanarwar, mutum 210 a cikin mutanen mata ne sai kuma 454 ‘yan kasashen waje ne.
Sanarwar ta ce kasar ta Nijar ta kasance tamkar wata hanya wadda masu safarar miyagun kwayoyin ke amfani da ita wurin safarar su zuwa kasashen Libiya da Aljeriya har zuwa kasashen Turai.
Hukumar ta kuma kara da cewa kaso 5.62 na wadanda aka kama shekarunsu ba su haura 18 ba sai kashi 58.92 sun kama daga 18 ne zuwa 29.
Hukumar ta ce tana yin iya bakin kokarinta domin dakile safarar miyagun kwayoyin, sai dai masu safarar suna fito da sabbin dabaru a kullum na kauce wa shingayen bincikensu.