Sport
Dollar
41,2837
0.12 %Euro
48,9712
-0.04 %Gram Gold
4.888,2000
-0.09 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hukumomi sun fara kama Abdul Razak Seidu ne ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 2025 da zinari da ya kai kilogiram 9.2 wanda kuɗinsa ya kai cedi miliyan 10.2.
Hukumar da ke kula da hakar zinari a Ghana (Goldbod) ta kama mutum uku da ake zargi da yin fasa-ƙaurin zinari da ya kimarsa ta kai cedi miliyan 100 daga ƙasar.
Da yake magana da manema labarai ranar Talata, shugaban hukumar Goldbod, Sammy Gyamfi, ya bayyana cewa mutanen suna cikin wata ƙungiya mai aikata laifuka da aka shafe makonni ana bincika tun lokacin da wani ɗan ƙasar ya fallasa ta ga hukumomi.
Mutanen da aka kama su ne: Abdul Razak Seidu da Bernard Nkrumah da Ibrahim Aremayew.
Hukumomi sun fara kama Abdul Razak Seidu ne a shataletalen Winnneba da ke Accra ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata da zinari da ya kai kilogiram 9.2 wanda kuɗinsa ya kai cedi miliyan 10.2.
Binciken da aka yi daga baya ya sa an kama Benard Nkrumah, wani mai sayen zinari da ke da laisisi da yake aiki a kamfanin NK Bernak Enterprise, wani abokin kasuwancin Rafmoh Gold Ltd, wanda masu bincike suka yi imanin cewa shi ya ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Comments
No comments Yet
Comment