Gaza ta binne Falasdinawa 80 a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah bayan da Isra'ila ta mayar da gawarwakin da ba a tantance ba - wasu a kammale, wasu kuwa gunduwa-gunduwa, a cewar wani jami'in asibiti.

Hotuna: Isra'ila ta mika wa Gaza gawarwaki 80 na Falasdinawa, wasu ma 'gunduwa-gunduwa'

An mayar da gawarwakin Falasdinawa kimanin 80 da sojojin Isra'ila suka kashe a lokacin farmakin da suka kai ta kasa zuwa Gaza tare da binne gawarwakin mutanen a makabartar Tel al Sultan, a cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta karbi gawarwakin a ranar Talata ta hanyar shingen Karem Abu Salem da ke karkashin ikon Isra'ila a kudancin Gaza, in ji wakilin Anadolu.

Ma’aikatan lafiya sanye da rigunan roba sun kwashe gawarwakin, wadanda aka lullube a shudiyen ledoji da aka rufe da zip, daga cikin motar daukar gawa. Daga nan ne aka kai gawarwakin a cikin wata babbar buldoza domin binne su a wani babban kabari.

Marwan al Hams, daraktan Asibitin Mohammed Yousef El-Najar da ke birnin Rafah, ya shaida wa Anadolu cewa, "Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da mu tun da farko kan dawo da gawarwakin wasu shahidai da dama zuwa Zirin Gaza, wadanda aka kiyasta cewa kimanin gawarwaki 80 ne." .

Al Hams ya kara da cewa, gawarwakin sun isa cikin wata kwantena, wasu a kammale, wasu gunduwa-gunduwa ne, wasu kuma sun ruɓe.

Al Hams ya ce an kai gawarwakin maƙabarta don binne su, sannan ma'aikatun lafiya da na shari'a za su yi bincike kan lamarin don gano yiwuwar ko an aikata "laifukan yaki" a kansu.

Hotunan jana'iazar suna da ban tsoro.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Wasu daga cikin gawarwakin sun rube an binne su a cikin babban kabarin, tun da ana fargabar cewa gawarwakin za su iya yaɗa cuta.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Sojojin Isra'ila sun kama Falasdinawa ne a lokacin farmakin da suka kai ta ƙasa, inda a yanzu suka miƙa gawarwakinsu ga hukumomin Gaza.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Wani jami’in asibitin ya ce, “Gawarwakin sun isa cikin wata kwantena, wasu a kammale, wasu gunduwa-gunduwa, wasu kuma sun ruɓe.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Ana sauke gawarwakin a cikin shuɗayen jakunkuna daga wata babbar mota, inda za a binne su a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza ranar 26 ga Disamban 2023.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Ba a gane ko su waye ba, kuma an binne su a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce adadin mutanen da suka mutu a yakin ya kai 20,915, tare da wasu dubbai da aka yi imanin sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Isra'ila ta aika da gawarwakin zuwa Gaza ta hanyar shingen Karem Abu Salem.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Kusan dukkanin mutanen Gaza miliyan 2.3 sun rasa matsugunansu a daya daga cikin yankunan da ke da yawan jama'a a duniya, kuma Isra'ila ta share kashi ɗaya cikin dari na al'ummar Gaza kafin yakin.

Falasdinawa sun gudanar da jana'izar mutane da yawa a makabartar Tel al Sultan da ke Rafah a Gaza a ranar 26 ga Disamban 2023, na Falasdinawa 80 da Isra'ila ta aike da gawarwakinsu zuwa Gaza. / Photo: AA

Yakin Isra'ila a Gaza na daya daga cikin hare-haren soji mafi muni a tarihin duniya a baya-bayan nan.

#