Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, wannan rana ta hadin kai ta kasa da kasa ta zo ne a wani babi mafi duhu a tarihin al'ummar Falasdinu.
Dubban mutane ne a fadin duniya suka gudanar da bikin ranar nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu a ranar Laraba, inda suka buƙaci a kawo karshen cin zarafin da Isra'ila ke yi kan al'ummar Falasdinawa, tare da yin kira da a samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a cikin wani sako ya ce "Wannan ranar hadin kai ta kasa da kasa ta zo ne a wani babi mafi duhu a tarihin al'ummar Falasdinu."
Guterres ya kuma yi nuni da wani muhimmin aiki na hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu, UNRWA, yana mai cewa a halin yanzu ya fi "muhimmanci fiye da kowane lokaci" cewa kasashen duniya su tsaya tare da hukumar a matsayin tushen tallafi ga al'ummar Falasdinu.
Masu fafutuka masu goyon bayan Falasdinu sun dinga ɗaga tutoci suna kira ga gwamnatin Burtaniya da ta bukaci a tsagaita wuta a Gaza da kuma dakatar da sayar da makamai ga Isra'ila, a gaban majalisar dokokin da ke gadar Westminster a London ranar 29 ga Nuwamba, 2023. (Palestine Action/Reel News/via Reuters)
Masu fafutuka na Philippines sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Quezon, Metro Manila, Philippines.
Wata yarinya tana rike da tutar Falasdinu don bikin ranar goyon bayan al'ummar Falasdinu, kusa da ginin ESCWA, a Beirut, Lebanon, a ranar 29 ga Nuwamba.
Mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu a Karachi, Pakistan a ranar 29 ga Nuwamba, 2023. / Hoto: Faizan Lakhani
Wani mai fafutuka mai goyon bayan Falasdinu ya rike wata alama da ke nuna hadin kai tare da mutane daga kabilu daban-daban na duniya, yayin da yake sanye da wata sutura ta asalin Amurka, a lokacin wata zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu da jam'iyyun siyasa daban-daban da kungiyoyin kwadago suka yi a Johannesburg a ranar 29 ga Nuwamba, 2023.
President Cyril Ramaphosa thanked Russian President Vladimir Putin for supporting South Africa’s G20 presidency and said bilateral trade could be expanded.
The government justified the location of the capital to Ciudad de la Paz by citing the space around it for expansion, but the moving-in process has been slow.