“Wajibi ne a hukunta wadanda suka aikata irin wadannan laifuffuka a karkashin dokokin kasa da kasa,” in ji shugaban kasar Turkiyya Erdogan a jawabinsa a taron sauyin yanayi na MDD na shekarar 2023 a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza a matsayin "laifi na yaƙi da cin zarafin bil'adama."
"Abin da ke faruwa a Gaza laifi ne na yaƙi, laifin cin zarafin bil'adama ne. Dole ne a hukunta wadanda suka aikata irin wadannan laifuka a karkashin dokokin kasa da kasa," in ji Shugaba Erdogan a jawabin da ya gabatar a wajen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2023 a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, (UAE) a ranar Juma'a.
A hare-haren da Isra'ila ta kai ta kashe Falasdinawa sama da 16,000, yawancinsu mata da kananan yara, kuma ba ta da wata hujja ta kare kanta a aikata hakan, in ji Erdogan.
Ya kara da cewa, Turkiyya na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya a duk cikin rikice-rikicen da ake fama da su, kuma tana kokarin samar da mafita mai adalci.