Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Jawabin nasa ya zo ne yayin da Turkiyya ke matsin lamba ga ƙasashen duniya don samar da lumana a Gaza da kuma tabbatar da cewa tsagaita wutar mai rauni tana ci gaba da wanzuwa a yayin da Isra’ila ke ci gaba da karya ta.
Ana ci gaba da tattaunawa kan kafa rundunar ayyuka ta ƙasa da ƙasa don aiki a Gaza, in ji Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, yana mai cewa tattaunawa na ci gaba da gudana kuma ana ta kokarin kammala komai.
"Batu ne mai matakai da yawa, don haka ana ci gaba da tattaunawa mai zurfi," Erdogan ya fada wa manema labarai a cikin jirginsa a ranar Juma'a, yayin dawo wa daga ziyarar da ya kai kasashen Kuwait, Qatar da Oman.
Ya ce "Mun shirya bayar da kowane irin tallafi, kuma aikinmu na shirye-shiryen na ci gaba."
Jawabin nasa ya zo ne yayin da Turkiyya ke matsin lamba ga ƙasashen duniya don samar da lumana a Gaza da kuma tabbatar da cewa tsagaita wutar mai rauni tana ci gaba da wanzuwa a yayin da Isra’ila ke ci gaba da karya ta.
"Hamas tana aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta kuma ta bayyana aniyarta a fili don yin hakan," in ji Erdogan. "Duk da haka, Isra'ila na ci gaba da karya ta. Dole ne ƙasashen duniya, musamman Amurka, su yi ƙoƙari sosai don tabbatar da cikakken aiki da yarjejeniyar daga bangaren Isra'ila."
Erdogan ya ce matsin lamba na diflomasiyya ga Isra'ila "yana da muhimmanci," ya ƙara da cewa takunkumi da dakatar da sayar da makamai na iya taimakawa wajen tilasta mata ta cika alkawuran da ta dauka.
Kokarin Turkiyya na ayyukan jinkai da sake gina Gaza
Erdogan ya yi alƙawarin cewa Turkiyya za ta ci gaba da ba da tallafin jin kai ba tare da katse wa ba ga Gaza, kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen sake gina yankin da yaƙi ya lalata.
"Gaza zai sake tashi - babu wanda ya kamata ya yi shakkar hakan," in ji shi. "Ba mu taɓa daina aika taimakonmu zuwa Masar ba, kuma za mu ci gaba da yin hakan."
Ya yi tsokaci da cewa Jirgen Ruwa na 17 na Turkiyya, wanda ke ɗauke da kayan agaji, ya isa tashar jiragen ruwa ta El-Arish da ke Masar kwanan nan. Ya ce hukumomin gwamnatin Turkiyya da ƙungiyoyi masu zaman kansu suna shirin taimaka wa wajen sake gina kayayyakin more rayuwa da aka lalata a Gaza.
"'Yan'uwanmu maza da mata na Gaza suna buƙatar komai saboda kawancen Isra'ila da bai dace ba," in ji Erdogan. "Yanzu lokaci ya yi da za a ɗauki mataki, ba magana a baki kawai ba."
Hadin kan yanki don sake gina Gaza
Erdogan ya ce ya tattauna batun farfadowar Gaza da shugabannin yankin Gulf a lokacin ziyartar yankin, inda ya kara da cewa Kuwait, Qatar da Oman duk sun nuna "ƙarfi da aniya mai kyau" don tallafawa sake gina yankin.
Ya ce, "Za mu sake gina Gaza tare." "Wannan ba wani abu bane da Turkiyya, Masar, ko kowace ƙasa a yankin Gulf za su iya yi su kaɗai - dole ne ya zama aiki na tare."
Ya yaba da goyon bayan da Qatar ta daɗe tana bai wa Falasɗinu, yana mai kiran Gaza "Zakaran Gwajin Dafin Duniyar Musulunci," kuma ya ce ministocin Turkiyya suna ci gaba da haɗin gwiwa da takwarorinsu na yankin.
Turkiyya ta shirya karbar bakuncin tattaunawar zaman lafiyar Ukraine
Da yake koma wa ga yaƙin Ukraine, Erdogan ya sake nanata shirin Turkiyya na karɓar bakuncin sabuwar tattaunawar zaman lafiya tsakanin Moscow da Kiev bayan rahotannin da ke cewa taron kolin Amurka da Rasha da aka shirya yi a Budapest ya tsaya.
"Wannan ya sake nuna muhimmancin hangen nesan Turkiyya game da zaman lafiya," in ji shi.
"Muna da kyakkyawar alaƙa da ɓangarorin biyu kuma mun sami amincewarsu. Wannan dama ce ta neman zaman lafiya, kuma mun ƙuduri aniyar amfani da wannan matsayi don amfanar da bil'adama."
Comments
No comments Yet
Comment