Kungiyar Hamas ta ce Isra'ilawa da dama sun mutu a harin 7 ga watan Oktoba ne sakamakon harbe-harben da sojoji da 'yan sandan Isra'ila suka yi musu bayan sun shiga rudani.

Hamas: 'Mamayar da Isra'ila ta yi mana ce ta tilasta kai mata hari a watan Oktoba'

Kungiyar fafutukar kare Falasdinawa ta Hamas ta ce harin ba-zata da ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba "wani mataki ne da ya wajaba" domin kare al'ummarta daga mamayar da Isra'ila ke yi musu.

Wannan "martani ne da ya dace na tunkarar dukkan kutungwilar da Isra'ila take kulla wa Falasdinawa," a cewar wani rahoto da kungiyar ta fitar.

Rahoton mai shafi 16 da Hamas ta fitar ranar Lahadi shi ne na farko da kungiyar ta fitar a harshen Turancin Ingilishi da Larabci, inda ta yi bayani kan dalilanta na kai wa Isa'ila harin ba-zata ta kan iyakarta da Gaza.

Ranar 7 ga watan Oktoba, daruruwan mayakan Hamas sun shiga Isra'ila ta kasa da sama da kuma ruwa.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutum 1,140, a cewar jami'an gwamnatin Isra'ila.

A lokacin harin, mayakan kungiyar sun yi garkuwa da kusan mutum 250, in ji wasu sabbin alkaluma da Isra'ila ta fitar.

Jami'an Isra'ila sun ce har yanzu akwai mutum kusan 132 da ake ci gaba da garkuwa da su a Gaza, cikinsu ana fargabar an kashe 27.

"Idan akwai wani rahoto na far wa fararen-hula, to an yi hakan ne ba da gangan ba kuma tabbas an yi hakan ne yayin gumurzu da dakarun mamaya," in ji rahoton na Hamas.

#