Ba za mu manta da wannan kisan kiyashin ba, kuma ba za mu bari a manta da shi ba. Ko ba dade ko ba jima dole Isra'ila sai ta girbe abin da ta shuka," in ji Shugaban Turkiyya.
Ci gaba da karya doka da Isra’ila ke yi a Gaza ya kara tabbatar da irin damuwar da muke da ita kan cewa Isra’ila “kasar ‘yan ta’adda ce”, kamar yadda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada matsayarsa game da Isra’ila.
“An samu damar samar da zaman lafiya sai dai abin takaici an rasa damar saboda hanya mai tsauri da Isra’ila ta dauka,” in ji Erdogan a lokacin da da yake hira da manema labarai a hanyarsa ta koma Turkiyya bayan taron Majalisar Dinkin Duniya kan Sauyin Yanayi da aka yi a Hadaddiyar Daular Larabawa.
“Tun da farko, mun sha bayyana cewa muna goyon bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin,” kamar yadda Erdogan ya bayyana cewa inda ya kara jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa domin ganin an samu zaman lafiya.
Kasashen Yamma da ke goyon bayan Isra’ila musamman Amurka da Birtaniya, sun ta kawo batun “barazanar Hamas” a matsayin abin tattaunawa maimakon tattauna batun mafitar samar da kasashe biyu wato two-state solution, kamar yadda Erdogan ya kara jaddadawa.
“Idan muka sa two-state solution a matsayin abin tattaunawa, matsalolin da suka shafi Gaza da kuma barazana a tsakaninsu za ta gushe,” kamar yadda ya kara da cewa. “Ficewar Hamas, ko kawar da Hamas, ba lamari ne mai yiwuwa ba.”
Kama Isra'ila da laifin kisan kiyashi
Dangane da karar da aka shigar kan Isra'ila a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Erdogan ya ce, Turkiyya na bibiyar shari'ar sosai, yana mai cewa: "Muna son a hukunta dukkan shugabannin Isra'ila da ke da hannu a wannan kisan kiyashi da kuma hukunta su."
Ba za mu manta da wannan kisan kiyashin ba, kuma ba za mu bari a manta da shi ba. Ko ba dade ko ba jima dole Isra'ila sai ta girbe abin da ta shuka," in ji Shugaban Turkiyya.