Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya bayyana irin kokarin da ake yi wajen shirya taron zaman lafiya na kasa da kasa a yayin  jawabinsa a taron kungiyar kasashe yankin Turkic a birnin Astana na kasar Kazakhstan.

Hadin kan kasashen da ke magana da Turkanci zai kawo zaman lafiya a rikicin Isra’ila da Falasdinu: Erdogan

Hadin kan kasashe yakin Turkic da ke magana da yaren Turkanci zai taimaka wajen samar da hanyar tsagaita wuta da zaman lafiya na dindindin a rikicin Isra'ila da Falasdinu, a cewar shugaban kasar Turkiyya.

"Babu wani abu da zai iya gaskata irin abubuwan da muka gani tun daga ranar 7 ga watan Oktoba," in ji Recep Tayyip Erdogan, yana mai magana kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza ba ƙaƙƙautawa.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a ranar Juma'a a taron kungiyar kasashe yankin Turkic a babban birnin Astana na kasar Kazakhstan.

"Babu wata kalma da za ta iya kwatanta irin wannan ta'asar, a tsawon kwanaki 28 da aka shafe ana aikata laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza."

Dangane da taimakon da Turkiyya ke bai wa Falasdinawa wadanda hare-haren Isra'ila ya shafa, Erdogan ya ce ya zuwa yanzu kasar ta aika da jiragen sama 10 dauke da kayan agaji zuwa Gaza, kuma za ta aike da ƙarin wasu idan bukatar yin hakan ya taso.

''Kokarin da muke yi na shirya taron zaman lafiya na ƙasa da ƙasa yana gudana,'' a cewar shugaban, yayin da yake magana kan irin matakan da Turkiyya ke dauka wajen kawo ƙarshen rikicin.

An soma babban taron kungiyar kasashen yankin Turkic (OST) karo na 10 ne a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar Juma'a.

A cewar kafar yada labarai ta gwamnatin shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, shugabannin kasashe da suka samu halartar taron sun hada da na Turkiyya da Azarbaijan da Hungary da Kyrgyzstan da Turkmenistan da kuma Uzbekistan.

Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da daukar matakan samar da zaman lafiya da ci gaba da kuma samar da tsaro ga daukacin kasashen yankin Turkic.

A makon nan ne sojojin Isra'ila suka zafafa kai hare-haren sama da na kasa a Gaza, yankin da ke fama da hare-haren wuce gona da iri tun bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ƙaddamar da wani harin ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

Kawo yanzu sama da mutum 10,500 aka kashe tun fara rikicin, daga ciki har da Falasdinawa a kalla 9,061.

#